Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66
  67. 67
  68. 68
  69. 69
  70. 70
  71. 71
  72. 72
  73. 73
  74. 74
  75. 75
  76. 76
  77. 77
  78. 78
  79. 79
  80. 80
  81. 81
  82. 82
  83. 83
  84. 84
  85. 85
  86. 86
  87. 87
  88. 88
  89. 89
  90. 90
  91. 91
  92. 92
  93. 93
  94. 94
  95. 95
  96. 96
  97. 97
  98. 98
  99. 99
  100. 100
  101. 101
  102. 102
  103. 103
  104. 104
  105. 105
  106. 106
  107. 107
  108. 108
  109. 109
  110. 110
  111. 111
  112. 112
  113. 113
  114. 114
  115. 115
  116. 116
  117. 117
  118. 118
  119. 119
  120. 120
  121. 121
  122. 122
  123. 123
  124. 124
  125. 125
  126. 126
  127. 127
  128. 128
  129. 129
  130. 130
  131. 131
  132. 132
  133. 133
  134. 134
  135. 135
  136. 136
  137. 137
  138. 138
  139. 139
  140. 140
  141. 141
  142. 142
  143. 143
  144. 144
  145. 145
  146. 146
  147. 147
  148. 148
  149. 149
  150. 150

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 84 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Sa Zuciya ga Haikali

1. Ina ƙaunar Haikalinka ƙwarai,Ya Allah Mai Iko Dukka!

2. A can nake so in kasance!Ina marmarin farfajiyar Haikalin Ubangiji.Da farin ciki mai yawa zan raira waƙa ga Allah Mai Rai.

3. Har ba'u ma sukan yi sheƙa,Tsattsewa suna da sheƙunansu,A kusa da bagadanka suke kiwon 'ya'yansu.Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina, Allahna.

4. Masu murna ne waɗanda suke zaune a Haikalinka,Kullum suna raira yabonka!

5. Masu murna ne waɗanda suka sami ƙarfinsu daga gare ka,Su waɗanda suka ƙosa su kai ziyara a Dutsen Sihiyona.

6. Sa'ad da suke ratsa busasshen kwari,Sai ya zama maɓuɓɓugar ruwa,Ruwan sama na farko yakan rufe wurin da tafkuna.

7. Sukan yi ta ƙara jin ƙarfi a cikin tafiyarsu,Za su kuwa ga Allahn alloli a Sihiyona!

8. Ka ji addu'ata, ya Ubangiji Allah Mai Runduna,Ka ji ni, ya Allah na Yakubu!

9. Duba, ya Allah, kai ne garkuwarmu,Ka dubi fuskar Sarkinmu, zaɓaɓɓenka.

10. Kwana guda da za a yi a Haikalinka,Ya fi kwana dubu da za a yi a wani wuri dabam.Na gwammace in tsaya a ƙofar Haikalin Allahna,Da in zauna a gidajen mugaye.

11. Ubangiji shi ne makiyayinmu, sarkinmu mai daraja,Yakan sa mana albarka, da alheri, da daraja,Ba ya hana kowane abu mai kyau ga waɗanda suke aikata abin da yake daidai.

12. Masu farin ciki ne waɗanda suka dogara gare ka,Ya Allah Mai Runduna!