Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66
  67. 67
  68. 68
  69. 69
  70. 70
  71. 71
  72. 72
  73. 73
  74. 74
  75. 75
  76. 76
  77. 77
  78. 78
  79. 79
  80. 80
  81. 81
  82. 82
  83. 83
  84. 84
  85. 85
  86. 86
  87. 87
  88. 88
  89. 89
  90. 90
  91. 91
  92. 92
  93. 93
  94. 94
  95. 95
  96. 96
  97. 97
  98. 98
  99. 99
  100. 100
  101. 101
  102. 102
  103. 103
  104. 104
  105. 105
  106. 106
  107. 107
  108. 108
  109. 109
  110. 110
  111. 111
  112. 112
  113. 113
  114. 114
  115. 115
  116. 116
  117. 117
  118. 118
  119. 119
  120. 120
  121. 121
  122. 122
  123. 123
  124. 124
  125. 125
  126. 126
  127. 127
  128. 128
  129. 129
  130. 130
  131. 131
  132. 132
  133. 133
  134. 134
  135. 135
  136. 136
  137. 137
  138. 138
  139. 139
  140. 140
  141. 141
  142. 142
  143. 143
  144. 144
  145. 145
  146. 146
  147. 147
  148. 148
  149. 149
  150. 150

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 65 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Yabo da Miƙa Hadaya ta Godiya

1. Ya Allah, dole mutane su yabe ka a Sihiyona,Tilas su ba ka abin da suka alkawarta.

2. Saboda kakan amsa addu'o'i,Dukan mutane za su zo wurinka.

3. Zunubanmu sun kāshe mu,Amma za ka gafarta zunubanmu.

4. Masu farin ciki ne waɗanda ka zaɓe suSu zauna a tsattsarkan wurinka!Za mu ƙoshi da kyawawan abubuwa da suke wurin zamanka,Da albarkun tsattsarkan Haikalinka!

5. Ka amsa mana, ya Allah Mai Cetonmu,Ka kuma cece mu ta wurin aikata al'amuran banmamaki.Mutane daga ko'ina a duniya,Har da waɗanda suke can nesa a hayin tekuna,Sun dogara gare ka.

6. Ka kakkafa duwatsu ta wurin ikonka,Ka bayyana ƙarfin ikonka.

7. Kakan kwantar da rurin tekuna,Kakan kwantar da rurin igiyar ruwa,Kakan kwantar da tarzomar jama'a.

8. Dukan duniya ta tsorata,Saboda manyan ayyuka da ka aikata.Ayyukanka sukan kawo sowa ta farin cikiDaga wannan iyakar duniya zuwa wancan.

9. Kakan nuna kana kulawa da ƙasar,Ta wurin aiko mata da ruwa.Ka arzuta ta, ta zama dausayi.Rafuffukan da ka bayar ba su taɓa ƙafewa ba,Sun sa ƙasar ta ba da amfanin gonaki,Abubuwan da ka aikata ke nan.

10. Ka kwarara ruwa mai yawa a gonakin da aka nome,Ka jiƙe su da ruwa,Ka tausasa ƙasar da yayyafi,Ka sa ƙananan tsire-tsire su yi girma.

11. Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka!Inda ka tafi duka akwai wadata!

12. Makiyaya suna cike da tumaki masu ƙiba,Tuddai kuma suna cike da farin ciki.

13. Sauruka suna cike da tumaki,Kwaruruka suna cike da alkama,Suna sowa suna raira waƙa ta farin ciki!