Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66
  67. 67
  68. 68
  69. 69
  70. 70
  71. 71
  72. 72
  73. 73
  74. 74
  75. 75
  76. 76
  77. 77
  78. 78
  79. 79
  80. 80
  81. 81
  82. 82
  83. 83
  84. 84
  85. 85
  86. 86
  87. 87
  88. 88
  89. 89
  90. 90
  91. 91
  92. 92
  93. 93
  94. 94
  95. 95
  96. 96
  97. 97
  98. 98
  99. 99
  100. 100
  101. 101
  102. 102
  103. 103
  104. 104
  105. 105
  106. 106
  107. 107
  108. 108
  109. 109
  110. 110
  111. 111
  112. 112
  113. 113
  114. 114
  115. 115
  116. 116
  117. 117
  118. 118
  119. 119
  120. 120
  121. 121
  122. 122
  123. 123
  124. 124
  125. 125
  126. 126
  127. 127
  128. 128
  129. 129
  130. 130
  131. 131
  132. 132
  133. 133
  134. 134
  135. 135
  136. 136
  137. 137
  138. 138
  139. 139
  140. 140
  141. 141
  142. 142
  143. 143
  144. 144
  145. 145
  146. 146
  147. 147
  148. 148
  149. 149
  150. 150

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 143 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Addu'ar Neman Ceto da Kiyayewa

1. Ya Ubangiji ka ji addu'ata,Ka kasa kunne ga roƙona!Kai adali ne mai aminci,Don haka ka amsa mini!

2. Ni bawanka, kada ka gabatar da ni a gaban shari'a,Gama ba wanda ba shi da laifi a gare ka.

3. Maƙiyina ya tsananta mini,Ya kore ni fata-fata.Ya sa ni a kurkuku mai duhu,Ina kama da waɗanda suka daɗe da mutuwa,

4. Don haka ina niyya in fid da zuciya,Ina cikin damuwa mai zurfi.

5. Na tuna kwanakin baya,Na tuna da dukan abin da ka yi,Na tuna da dukan ayyukanka.

6. Na ɗaga hannuwana sama, ina addu'a gare ka,Kamar busasshiyar ƙasa, raina yana jin ƙishinka.

7. Yanzu ka amsa mini, ya Ubangiji!Na fid da zuciya duka!Kada ka ɓuya mini,Don kada in zama cikin waɗanda suke gangarawa zuwa lahira.

8. A gare ka nake dogara,Da safe ka tuna mini da madawwamiyar ƙaunarka.Addu'ata ta hau zuwa gare ka,Ka nuna mini hanyar da zan bi.

9. Na tafi wurinka don ka kiyaye ni, ya Ubangiji,Ka cece ni daga maƙiyana.

10. Kai ne Allahna,Ka koya mini in aikata nufinka.Ka sa in sami alherin Ruhunka.Ka bi da ni a hanyar lafiya.

11. Ka cece ni, ya Ubangiji, kamar yadda ka alkawarta.Saboda alherinka ka tsamo ni daga wahalaina!

12. Saboda ƙaunar da kake yi mini,Ka kashe maƙiyana.Ka hallakar da dukan waɗanda suke zaluntata.Gama ni bawanka ne.