Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66
  67. 67
  68. 68
  69. 69
  70. 70
  71. 71
  72. 72
  73. 73
  74. 74
  75. 75
  76. 76
  77. 77
  78. 78
  79. 79
  80. 80
  81. 81
  82. 82
  83. 83
  84. 84
  85. 85
  86. 86
  87. 87
  88. 88
  89. 89
  90. 90
  91. 91
  92. 92
  93. 93
  94. 94
  95. 95
  96. 96
  97. 97
  98. 98
  99. 99
  100. 100
  101. 101
  102. 102
  103. 103
  104. 104
  105. 105
  106. 106
  107. 107
  108. 108
  109. 109
  110. 110
  111. 111
  112. 112
  113. 113
  114. 114
  115. 115
  116. 116
  117. 117
  118. 118
  119. 119
  120. 120
  121. 121
  122. 122
  123. 123
  124. 124
  125. 125
  126. 126
  127. 127
  128. 128
  129. 129
  130. 130
  131. 131
  132. 132
  133. 133
  134. 134
  135. 135
  136. 136
  137. 137
  138. 138
  139. 139
  140. 140
  141. 141
  142. 142
  143. 143
  144. 144
  145. 145
  146. 146
  147. 147
  148. 148
  149. 149
  150. 150

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Mulkin Sarkin da Ubangiji Ya Zaɓa

1. Don me al'ummai suke shirin tayarwa?Don me waɗannan mutane suke ƙulla shawarwarin banza?

2. Sarakunan duniya sun yi tayarwa,Masu mulkinsu suna shirya maƙarƙashiya tare,Gāba da Ubangiji da zaɓaɓɓen sarkinsa.

3. Suna cewa, “Bari mu 'yantar da kanmu daga mulkinsu,Bari mu fice daga ƙarƙashinsu!”

4. Ubangiji ya yi dariya daga kan kursiyinsa can Sama,Ya mai da su abin dariya.

5. Ya yi musu magana da fushi,Ya razanar da su da hasalarsa,

6. Ya ce, “A bisa Sihiyona, dutsena tsattsarka,Na naɗa sarkina.”

7. Sarkin ya ce, “Zan yi shelar abin da Ubangiji ya hurta.Ubangiji ya ce mini, ‘Kai ɗana ne,Yau ne na zama mahaifinka.

8. Ka yi roƙo, zan kuwa ba ka dukan al'ummai,Dukan duniya kuma za ta zama taka.

9. Za ka mallake su da sandan ƙarfe,Za ka farfashe su kamar tukunyar yumɓu.’ ”

10. Yanzu ku kasa kunne gare ni, ku sarakuna,Ku mai da hankali, ku mahukunta!

11. Ku bauta wa Ubangiji da tsoro,Ku yi rawar jiki, ku rusuna masa,

12. Ku yi mubaya'a da Ɗan,Idan kuwa ba haka ba zai yi fushi da ku, za ku kuwa mutu,Gama yakan yi fushi da sauri.Albarka ta tabbata ga dukan masu zuwa gare shi neman mafaka!