Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66
  67. 67
  68. 68
  69. 69
  70. 70
  71. 71
  72. 72
  73. 73
  74. 74
  75. 75
  76. 76
  77. 77
  78. 78
  79. 79
  80. 80
  81. 81
  82. 82
  83. 83
  84. 84
  85. 85
  86. 86
  87. 87
  88. 88
  89. 89
  90. 90
  91. 91
  92. 92
  93. 93
  94. 94
  95. 95
  96. 96
  97. 97
  98. 98
  99. 99
  100. 100
  101. 101
  102. 102
  103. 103
  104. 104
  105. 105
  106. 106
  107. 107
  108. 108
  109. 109
  110. 110
  111. 111
  112. 112
  113. 113
  114. 114
  115. 115
  116. 116
  117. 117
  118. 118
  119. 119
  120. 120
  121. 121
  122. 122
  123. 123
  124. 124
  125. 125
  126. 126
  127. 127
  128. 128
  129. 129
  130. 130
  131. 131
  132. 132
  133. 133
  134. 134
  135. 135
  136. 136
  137. 137
  138. 138
  139. 139
  140. 140
  141. 141
  142. 142
  143. 143
  144. 144
  145. 145
  146. 146
  147. 147
  148. 148
  149. 149
  150. 150

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 74 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Addu'ar Neman Ceton Al'ummar Allah

1. Don me ka yashe mu haka, ya Allah?Za ka yi ta fushi da jama'arka har abada ne?

2. Ka tuna da jama'arka waɗanda ka zaɓa su zama naka tuntuni,Ka tuna da jama'arka waɗanda ka fansa,Don su zama kabilarka.Ka tuna da Dutsen Sihiyona, inda zatinka yake!

3. Ka zo, ka yi yawo a wannan kufai,Abokan gābanmu sun lalatar da kome na cikin Haikali!

4. Abokan gābanka suka yi sowa ta nasaraA inda akan sadu da kai,Sun ƙwace Haikalin.

5. Suna kama da masu saran itace,Suna saran itatuwa da gaturansu.

6. Da gaturansu da gudumarsu,Sun ragargaje ƙyamaren da aka yi da katako.

7. Sun sa wa Haikalinka wuta,Sun ƙazantar da wurin da akan yi maka sujada,Sun farfashe shi duk.

8. Sun yi niyya su murƙushe mu sarai,Sun ƙone kowane tsattsarkan wuri na ƙasar.

9. Ba sauran tsarkakan alamu,Ba sauran annabawan da suka ragu,Ba kuwa wanda ya san ƙarewar wannan.

10. Ya Allah, har yaushe abokan gābanmu za su yi ta yi mana ba'a?Za su yi ta zargin sunanka har abada ne?

11. Me ya sa ka ƙi taimakonmu?Ka tasar musu ka hallaka su!

12. Amma ya Allah, kai ne Sarkinmu tun daga farko,Ka yi nasara da duniya.

13. Da ƙarfin ikonka ka raba teku,Ka farfashe kawunan dodannin ruwa,

14. Ka ragargaje kawunan kadduna,Ka kuwa ba mutanen hamada su ci.

15. Ka sa ruwan maɓuɓɓugai ya yi gudu,Ka sa manyan koguna su ƙafe.

16. Ka halicci yini da dare,Ka sa rana da wata a wurarensu.

17. Ka yi wa duniya kan iyaka,Ka kuwa yi lokatan damuna da na rani.

18. Amma ka tuna fa, ya Ubangiji, abokan gābanka suna yi maka ba'a,Su wawaye ne waɗanda suke raina ka.

19. Kada ka ba da jama'arka marasa taimakoA hannun mugayen maƙiyansu,Kada ka manta da jama'arka waɗanda ake tsananta musu!

20. Ka tuna da alkawarin da ka yi mana,Akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar!

21. Kada ka bari a kori waɗanda ake zalunta,Amma bari matalauta da masu mayata su yabe ka.

22. Ka tashi, ya Allah, ka kāre kanka!Ka tuna fa, marasa tsoronka suna ta yi maka ba'a dukan yini!

23. Kada ka manta da hargowar maƙiyanka,Kada ka manta da hayaniyar da magabtanka suke ta yi.