Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66
  67. 67
  68. 68
  69. 69
  70. 70
  71. 71
  72. 72
  73. 73
  74. 74
  75. 75
  76. 76
  77. 77
  78. 78
  79. 79
  80. 80
  81. 81
  82. 82
  83. 83
  84. 84
  85. 85
  86. 86
  87. 87
  88. 88
  89. 89
  90. 90
  91. 91
  92. 92
  93. 93
  94. 94
  95. 95
  96. 96
  97. 97
  98. 98
  99. 99
  100. 100
  101. 101
  102. 102
  103. 103
  104. 104
  105. 105
  106. 106
  107. 107
  108. 108
  109. 109
  110. 110
  111. 111
  112. 112
  113. 113
  114. 114
  115. 115
  116. 116
  117. 117
  118. 118
  119. 119
  120. 120
  121. 121
  122. 122
  123. 123
  124. 124
  125. 125
  126. 126
  127. 127
  128. 128
  129. 129
  130. 130
  131. 131
  132. 132
  133. 133
  134. 134
  135. 135
  136. 136
  137. 137
  138. 138
  139. 139
  140. 140
  141. 141
  142. 142
  143. 143
  144. 144
  145. 145
  146. 146
  147. 147
  148. 148
  149. 149
  150. 150

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 51 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Addu'ar Roƙon Gafara

1. Ka yi mini jinƙai, ya Allah,Sabili da madawwamiyar ƙaunarka.Ka shafe zunubaina,Saboda jinƙanka mai girma!

2. Ka wanke muguntata sarai,Ka tsarkake ni daga zunubina!

3. Na gane laifina,Kullum ina sane da zunubina.

4. Na yi maka zunubi, kai kaɗai na yi wa,Na kuwa aikata mugunta a gare ka.Daidai ne shari'ar da ka yi mini,Daidai ne ka hukunta ni.

5. Mugu ne ni tun lokacin da aka haife ni,Mai zunubi ne ni tun daga ranar da aka haife ni.

6. Amintacciyar zuciya ita kake so,Ka cika tunanina da hikimarka.

7. Ka kawar da zunubina, zan kuwa tsarkaka,Ka wanke ni, zan kuwa fi auduga fari.

8. Bari in ji sowa ta farin ciki da murna.Ko da yake ka ragargaza ni,Ka kakkarya ni, duk da haka zan sāke yin murna.

9. Ka kawar da fuskarka daga zunubaina,Ka shafe duk muguntata.

10. Ka halitta tsarkakakkiyar zuciya a cikina, ya Allah,Ka sa sabon halin biyayya a cikina.

11. Kada ka kore ni daga gabanka,Kada ka ɗauke mini Ruhunka Mai Tsarki.

12. Ka sāke mayar mini da farin ciki na cetonka,Ka ƙarfafa ni da zuciya ta biyayya.

13. Sa'an nan zan koya wa masu zunubi umarnanka,Za su kuwa komo wurinka.

14. Ka rayar da raina, ya Allah Mai Cetona,Zan kuwa yi shelar adalcinka da farin ciki.

15. Ka taimake ni in yi magana, ya Ubangiji,Zan kuwa yabe ka.

16. Ba ka son sadakoki, ai, da na ba ka,Ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.

17. Hadayata, ita ce halin ladabi, ya Allah,Zuciya mai ladabi da biyayya,Ba za ka ƙi ba, ya Allah.

18. Ya Allah, ka yi wa Sihiyona alheri, ka taimake ta,Ka sāke gina garun Urushalima.

19. Sa'an nan za ka ji daɗin hadaya ta ainihi,Da dukan hadayun ƙonawa.Za a miƙa bijimai hadayu a bisa bagadenka.