Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66
  67. 67
  68. 68
  69. 69
  70. 70
  71. 71
  72. 72
  73. 73
  74. 74
  75. 75
  76. 76
  77. 77
  78. 78
  79. 79
  80. 80
  81. 81
  82. 82
  83. 83
  84. 84
  85. 85
  86. 86
  87. 87
  88. 88
  89. 89
  90. 90
  91. 91
  92. 92
  93. 93
  94. 94
  95. 95
  96. 96
  97. 97
  98. 98
  99. 99
  100. 100
  101. 101
  102. 102
  103. 103
  104. 104
  105. 105
  106. 106
  107. 107
  108. 108
  109. 109
  110. 110
  111. 111
  112. 112
  113. 113
  114. 114
  115. 115
  116. 116
  117. 117
  118. 118
  119. 119
  120. 120
  121. 121
  122. 122
  123. 123
  124. 124
  125. 125
  126. 126
  127. 127
  128. 128
  129. 129
  130. 130
  131. 131
  132. 132
  133. 133
  134. 134
  135. 135
  136. 136
  137. 137
  138. 138
  139. 139
  140. 140
  141. 141
  142. 142
  143. 143
  144. 144
  145. 145
  146. 146
  147. 147
  148. 148
  149. 149
  150. 150

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Gādon Alheri

1. Ya Allah, ka kiyaye ni, gama na zo gare ka neman mafaka.

2. Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Ubangijina,Dukan kyawawan abubuwan da nake da suDaga gare ka suke.”

3. Dubi irin martabar da amintattun jama'ar Ubangiji suke da ita!Ba abin da raina ya fi so,Sai in zauna tare da su.

4. Waɗanda suke hanzari zuwa ga gumaka,Za su jawo wa kansu wahala.Ba zan yi tarayya da su da hadayarsu ba.Ba zan yi sujada ga gumakansu ba.

5. Kai ne kaɗai, nake da shi, ya Ubangiji,Kai ne kake biyan dukan bukatata,Raina yana hannunka.

6. Kyautanka zuwa gare ni da bansha'awa suke,Kyawawa ne kuwa ƙwarai!

7. Na yabi Ubangiji saboda yana bi da ni,Da dare kuma lamirina yana yi mini fadaka.

8. A kullum ina jin Ubangiji yana tare da ni,Yana nan kusa, ba abin da zai girgiza ni.

9. Don haka cike nake da murna da farin ciki,Kullum kuwa ina jin kome lafiya yake,

10. Saboda ba za ka yarda in shiga lahira ba,Ba za ka bar wanda kake ƙauna a zurfafa daga ƙarƙas ba.

11. Za ka nuna mini hanyar rai,Kasancewarka takan sa in cika da farin ciki,Taimakonka kuwa yana kawo jin daɗi har abada.