Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66
  67. 67
  68. 68
  69. 69
  70. 70
  71. 71
  72. 72
  73. 73
  74. 74
  75. 75
  76. 76
  77. 77
  78. 78
  79. 79
  80. 80
  81. 81
  82. 82
  83. 83
  84. 84
  85. 85
  86. 86
  87. 87
  88. 88
  89. 89
  90. 90
  91. 91
  92. 92
  93. 93
  94. 94
  95. 95
  96. 96
  97. 97
  98. 98
  99. 99
  100. 100
  101. 101
  102. 102
  103. 103
  104. 104
  105. 105
  106. 106
  107. 107
  108. 108
  109. 109
  110. 110
  111. 111
  112. 112
  113. 113
  114. 114
  115. 115
  116. 116
  117. 117
  118. 118
  119. 119
  120. 120
  121. 121
  122. 122
  123. 123
  124. 124
  125. 125
  126. 126
  127. 127
  128. 128
  129. 129
  130. 130
  131. 131
  132. 132
  133. 133
  134. 134
  135. 135
  136. 136
  137. 137
  138. 138
  139. 139
  140. 140
  141. 141
  142. 142
  143. 143
  144. 144
  145. 145
  146. 146
  147. 147
  148. 148
  149. 149
  150. 150

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 81 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Waƙar Idi

1. Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah Mai Cetonmu,Ku raira yabbai ga Allah na Yakubu!

2. A fara waƙa, ku buga bandiri,Ku yi waƙoƙi masu daɗi da molaye, da garayu.

3. Ku busa ƙaho domin idin,A amaryar wata,Da a tsakiyar farin wata.

4. Wannan doka ce a Isra'ila,Umarni ne kuma daga Allah na Yakubu.

5. Ya ba da wannan umarni ga jama'ar Isra'ila,A lokacin da ya fita gāba da ƙasar Masar.Na ji wata murya da ban saba ji ba tana cewa,

6. “Na ɗauke muku kayayyaki masu nauyi da kuke ɗauke da su a kā,Na sa kuka ajiye kwandunan aikinku.

7. Sa'ad da kuke shan wahalaKuka yi kira a gare ni, na kuwa cece ku.Daga maɓuyata cikin hadiri, na amsa muku,Na jarraba ku a maɓuɓɓugan Meriba.

8. “Ya kuma jama'ata Isra'ila ku kasa kunne,Ina kuwa so ku saurara gare ni.

9. Faufau kada ku bauta wa gumaka,Ko ku yi sujada ga wanina.

10. Ni ne Ubangiji Allahnku,Wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar.Ku buɗe bakinku, zan ciyar da ku.

11. “Amma jama'ata ba su kasa kunne gare ni ba.Isra'ila ta ƙi yi mini biyayya.

12. Saboda haka na bar su su yi ta kangarewarsu,Su aikata duk irin abin da suka ga dama.

13. Ina kuwa so jama'ata su kasa kunne gare ni,Su kuwa yi mini biyayya!

14. Da sai in kori abokan gābansu nan da nan,In yi nasara da dukan maƙiyansu.

15. Maƙiyana, za su sunkuya a gabana saboda tsoro,Hukuncinsu na har abada ne.

16. Zan ciyar da ku da kyakkyawar alkama,In ƙosar da ku da zuma.”