Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66
  67. 67
  68. 68
  69. 69
  70. 70
  71. 71
  72. 72
  73. 73
  74. 74
  75. 75
  76. 76
  77. 77
  78. 78
  79. 79
  80. 80
  81. 81
  82. 82
  83. 83
  84. 84
  85. 85
  86. 86
  87. 87
  88. 88
  89. 89
  90. 90
  91. 91
  92. 92
  93. 93
  94. 94
  95. 95
  96. 96
  97. 97
  98. 98
  99. 99
  100. 100
  101. 101
  102. 102
  103. 103
  104. 104
  105. 105
  106. 106
  107. 107
  108. 108
  109. 109
  110. 110
  111. 111
  112. 112
  113. 113
  114. 114
  115. 115
  116. 116
  117. 117
  118. 118
  119. 119
  120. 120
  121. 121
  122. 122
  123. 123
  124. 124
  125. 125
  126. 126
  127. 127
  128. 128
  129. 129
  130. 130
  131. 131
  132. 132
  133. 133
  134. 134
  135. 135
  136. 136
  137. 137
  138. 138
  139. 139
  140. 140
  141. 141
  142. 142
  143. 143
  144. 144
  145. 145
  146. 146
  147. 147
  148. 148
  149. 149
  150. 150

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Kewar Allah a Baƙuwar Ƙasa

1. Kamar yadda kishimi yake marmarin ruwan sanyi daga rafi,Haka nake marmarinka, ya Allah.

2. Ina jin ƙishinka, ya Allah, ya Allah Mai Rai,Yaushe zan tafi in yi sujada a gabanka?

3. Dare da rana ina kuka,Hawayena kaɗai su ne abincina,A kowane lokaci maƙiyana suna ta tambayata,“Ina Allahnka?”

4. Zuciyata takan ɓaci in na tuna da abin da ya wuce,Sa'ad da nakan tafi tare da taron jama'a zuwa Haikalin Allah,Ina bishe su a jere.Taron jama'a masu farin ciki, suna raira waƙa,Suna ta da murya, suna yabon Allah.

5. Me ya sa nake baƙin ciki haka?Me ya sa nake damuwa ƙwarai?Zan dogara ga Allah,Zan sāke yin yabonsa,Mai Cetona, Allahna.

6. Zuciyata ta karaiSaboda haka zan tuna da kaiA wajen Urdun, da kusa da Dutsen Harmon, da na Mizar,Zan tuna da kai.

7. Zurfafan tekuna suna kiran junansu,Matsirgar ruwa na Allah kuwa suna ta ruri!Igiyoyin ruwa na baƙin cikiSuka yi wa raina ambaliya.

8. Ubangiji ya nuna madawwamiyar ƙaunarsa kowace rana!Ni ma in raira yabo gare shi kowane dare,In yi addu'a ga Allah, wanda ya ba ni rai.

9. Ga Allah wanda yake tsarona na ce,“Me ya sa ka manta da ni?Me ya sa nake ta shan wahalaSaboda muguntar maƙiyana?”

10. An ragargaza ni da zargin maƙiyanaWaɗanda suke tambayata kullum,“Ina Allahnka?”

11. Me ya sa ni ɓacin rai haka?Me ya sa ni damuwa?Zan dogara ga Allah.Har yanzu ma zan yabe shi,Mai Cetona, Allahna.