Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66
  67. 67
  68. 68
  69. 69
  70. 70
  71. 71
  72. 72
  73. 73
  74. 74
  75. 75
  76. 76
  77. 77
  78. 78
  79. 79
  80. 80
  81. 81
  82. 82
  83. 83
  84. 84
  85. 85
  86. 86
  87. 87
  88. 88
  89. 89
  90. 90
  91. 91
  92. 92
  93. 93
  94. 94
  95. 95
  96. 96
  97. 97
  98. 98
  99. 99
  100. 100
  101. 101
  102. 102
  103. 103
  104. 104
  105. 105
  106. 106
  107. 107
  108. 108
  109. 109
  110. 110
  111. 111
  112. 112
  113. 113
  114. 114
  115. 115
  116. 116
  117. 117
  118. 118
  119. 119
  120. 120
  121. 121
  122. 122
  123. 123
  124. 124
  125. 125
  126. 126
  127. 127
  128. 128
  129. 129
  130. 130
  131. 131
  132. 132
  133. 133
  134. 134
  135. 135
  136. 136
  137. 137
  138. 138
  139. 139
  140. 140
  141. 141
  142. 142
  143. 143
  144. 144
  145. 145
  146. 146
  147. 147
  148. 148
  149. 149
  150. 150

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 45 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Waƙar Ɗaurin Auren Sarki

1. Kwanyata ta cika da kyawawan kalmomi,Lokacin da nake tsara waƙar sarki,Harshena kuwa kamar alkalami ne na ƙwararren marubuci.

2. Kai ne mafi kyau a cikin dukan mutane,Kai mai kyakkyawan lafazi ne,Kullum Allah yakan sa maka albarka!

3. Ka sha ɗamara da takobinka, ya Maɗaukakin Sarki,Kai mai iko ne, Maɗaukaki!

4. Ka yi hawan ɗaukaka zuwa nasara,Domin ka tsare gaskiya da adalci.Saboda ikonka za ka yi babban rinjaye.

5. Kibanka suna da tsini,Suna huda zuciyar abokan gābanka,Al'ummai suna fāɗuwa ƙasa a ƙafafunka.

6. Kursiyinka, ya Allah, zai dawwama har abada abadin!Kana mulkin mallakarka da adalci.

7. Kana ƙaunar abin da yake daidai,Kana ƙin abin da yake mugu.Saboda haka Allah, Allahnka, ya zaɓe ka,Ya kuwa kwararo maka farin ciki mai yawa fiye da kowa.

8. Tufafinka suna ƙanshin turaren mur, da na aloyes, da na kashiya,A kowace fādar hauren giwa, mawaƙa suna yi maka waƙar.

9. Daga cikin matan da suke fadarka, har da 'ya'yan sarakuna.A daman kursiyinka kuwa ga sarauniya a tsaye.Tana saye da kayan ado na zinariya mafi kyau duka.

10. Ki ji abin da zan faɗa, ya ke amaryar sarki,Ki manta da mutanenki da danginki.

11. Saboda ke kyakkyawa ce sarki zai so ki,Shi ne maigidanki, sai ki yi masa biyayya.

12. Mutanen Taya za su kawo miki kyautai,Attajirai za su zo su sami farin jini a gare ki.

13. Gimbiya tana fāda, kyakkyawa ce ainun,Da zaren zinariya aka saƙa rigarta,

14. Aka kai ta wurin sarki tana saye da riga mai ado.Ga 'yan matanta a biye,Aka kawo su wurin sarki.

15. Da farin ciki da murna suka zo,Suka shiga fādar sarki.

16. Za ka haifi 'ya'ya maza da yawa,Waɗanda za su maye matsayin kakanninka,Za ka sa su zama masu mulkin duniya duka.

17. Waƙata za ta sa a yi ta tunawa da sunanka har abada,Dukan jama'a za su yabe ka a dukan zamanai masu zuwa.