Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66
  67. 67
  68. 68
  69. 69
  70. 70
  71. 71
  72. 72
  73. 73
  74. 74
  75. 75
  76. 76
  77. 77
  78. 78
  79. 79
  80. 80
  81. 81
  82. 82
  83. 83
  84. 84
  85. 85
  86. 86
  87. 87
  88. 88
  89. 89
  90. 90
  91. 91
  92. 92
  93. 93
  94. 94
  95. 95
  96. 96
  97. 97
  98. 98
  99. 99
  100. 100
  101. 101
  102. 102
  103. 103
  104. 104
  105. 105
  106. 106
  107. 107
  108. 108
  109. 109
  110. 110
  111. 111
  112. 112
  113. 113
  114. 114
  115. 115
  116. 116
  117. 117
  118. 118
  119. 119
  120. 120
  121. 121
  122. 122
  123. 123
  124. 124
  125. 125
  126. 126
  127. 127
  128. 128
  129. 129
  130. 130
  131. 131
  132. 132
  133. 133
  134. 134
  135. 135
  136. 136
  137. 137
  138. 138
  139. 139
  140. 140
  141. 141
  142. 142
  143. 143
  144. 144
  145. 145
  146. 146
  147. 147
  148. 148
  149. 149
  150. 150

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Ayyukan Allah da Shari'arsa

1. Dubi yadda sararin sama yake bayyana ɗaukakar Allah!Dubi yadda suke bayyana a fili ayyukansa da ya yi!

2. Kowace rana tana shelar ɗaukakarsa ga ranar da take biye,Kowane dare yana nanata ɗaukakarsa ga daren da take biye.

3. Ba magana ko kalma da aka hurta,Ba wani amon da aka ji,

4. Duk da haka muryarsu ta game duniya duka,Saƙonsu ya kai ko'ina a duniya.Allah ya kafa wa rana alfarwa a sararin sama,

5. Tana fitowa kamar ango yana taƙama daga gidansa,Kamar ɗan wasan da ya ƙosa ya yi tsere.

6. Takan fara daga wannan ƙarshen sararin sama, ta kewaye zuwa wancan.Ba abin da zai iya ɓuya daga zafinta.

7. Dokar Ubangiji cikakkiya ce,Tana wartsakar da rai.Umarnan Ubangiji abin dogara ne,Sukan ba da hikima ga wanda ba shi da ita.

8. Ka'idodin Ubangiji daidai suke,Waɗanda suke biyayya da su sun ji daɗi.Umarnan Ubangiji daidai suke,Sukan ba da fahimi ga zuciya.

9. Daidai ne a bauta wa Ubangiji,A ci gaba da yi har abada.Duk abin da Ubangiji ya hukunta daidai ne,A kullum hukuntan Ubangiji daidai suke.

10. Abin da ake so ne fiye da zinariya,I, fiye da tatacciyar zinariya ma,Sun fi zuma zaƙi,I, fiye da tatacciyar zuma ma.

11. Suna ba ni ilimi, ni baranka,Ina samun ladan yin biyayya da su.

12. Ba mai iya ganin kuskuren kansa,Ka cece ni daga ɓoyayyun laifofi!

13. Ka tsare ni kuma daga laifofi na fili,Kada ka bari su mallake ni.Sa'an nan zan zama kamili,In kuɓuta daga mugun zunubi.

14. Ka sa maganata da tunanina su zama abin karɓa a gare ka,Ya Ubangiji, Mafakata da Mai Fansata!