Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66
  67. 67
  68. 68
  69. 69
  70. 70
  71. 71
  72. 72
  73. 73
  74. 74
  75. 75
  76. 76
  77. 77
  78. 78
  79. 79
  80. 80
  81. 81
  82. 82
  83. 83
  84. 84
  85. 85
  86. 86
  87. 87
  88. 88
  89. 89
  90. 90
  91. 91
  92. 92
  93. 93
  94. 94
  95. 95
  96. 96
  97. 97
  98. 98
  99. 99
  100. 100
  101. 101
  102. 102
  103. 103
  104. 104
  105. 105
  106. 106
  107. 107
  108. 108
  109. 109
  110. 110
  111. 111
  112. 112
  113. 113
  114. 114
  115. 115
  116. 116
  117. 117
  118. 118
  119. 119
  120. 120
  121. 121
  122. 122
  123. 123
  124. 124
  125. 125
  126. 126
  127. 127
  128. 128
  129. 129
  130. 130
  131. 131
  132. 132
  133. 133
  134. 134
  135. 135
  136. 136
  137. 137
  138. 138
  139. 139
  140. 140
  141. 141
  142. 142
  143. 143
  144. 144
  145. 145
  146. 146
  147. 147
  148. 148
  149. 149
  150. 150

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 62 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Allah ne kaɗai Mafaka

1. Ga Allah kaɗai na dogara,Cetona daga gare shi yake fitowa.

2. Shi kaɗai ne mai kiyaye ni, Mai Cetona,Shi ne kariyata,Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam.

3. Har yaushe dukanku za ku fāɗa wa wani don ku yi nasara da shi,Kamar rusasshen garu,Ko kuma dangar da ta fāɗi?

4. Ba abin da kuke so, sai ku ƙasƙantar da shi daga maƙaminsa na daraja,Kuna jin daɗin yin ƙarairayi.Kuna sa masa albarka,Amma a zuciyarku la'antarwa kuke yi.

5. Ga Allah kaɗai na dogara,A gare shi na sa zuciyata.

6. Shi kaɗai ne mai kiyaye ni, Mai Cetona,Shi ne kariyata,Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam.

7. Cetona da darajata daga Allah ne,Shi ne ƙaƙƙarfan makiyayina,Shi ne mafakata.

8. Ya jama'ata, ku dogara ya Allah a kowane lokaci!Ku faɗa masa dukan wahalarku,Gama shi ne mafakarmu.

9. Talakawa kamar shaƙar numfashi suke,Manyan mutane, su ma haka suke marasa amfani.Ko an auna su a ma'auni, sam ba su da nauyin kome,Sun fi numfashi shakaf.

10. Kada ku dogara da aikin kama-karya.Kada ku sa zuciya za ku ci ribar kome ta wurin fashi.In kuwa dukiyarku ta ƙaru,Kada ku dogara gare ta.

11. Sau ɗaya Allah ya faɗa,Sau biyu na ji, cewa Allah yake da iko.

12. Madawwamiyar ƙauna, ta Ubangiji ce.Kai kanka, ya Ubangiji, kake sāka waKowane mutum bisa ga ayyukansa.