1. Ka cece ni ta wurin ikonka, ya Allah,Ka cece ni ta wurin ƙarfinka!
2. Ka ji addu'ata, ya Allah,Ka saurari kalmomina!
3. Masu girmankai sun tasar mini,Mugaye suna nema su kashe ni,Mutanen da ba su kula da Allah ba.
4. Na sani Allah ne mai taimakona,Na sani Ubangiji shi ne mai tsarona!
5. Ubangiji ya hukunta wa maƙiyana da irin muguntarsu!Gama zai hallaka su saboda shi mai aminci ne.
6. Da murna zan miƙa maka hadaya,Zan yi maka godiya, ya Ubangiji,Domin kai mai alheri ne.
7. Ka cece ni daga dukan wahalaina,Na kuwa ga an kori maƙiyana.