Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66
  67. 67
  68. 68
  69. 69
  70. 70
  71. 71
  72. 72
  73. 73
  74. 74
  75. 75
  76. 76
  77. 77
  78. 78
  79. 79
  80. 80
  81. 81
  82. 82
  83. 83
  84. 84
  85. 85
  86. 86
  87. 87
  88. 88
  89. 89
  90. 90
  91. 91
  92. 92
  93. 93
  94. 94
  95. 95
  96. 96
  97. 97
  98. 98
  99. 99
  100. 100
  101. 101
  102. 102
  103. 103
  104. 104
  105. 105
  106. 106
  107. 107
  108. 108
  109. 109
  110. 110
  111. 111
  112. 112
  113. 113
  114. 114
  115. 115
  116. 116
  117. 117
  118. 118
  119. 119
  120. 120
  121. 121
  122. 122
  123. 123
  124. 124
  125. 125
  126. 126
  127. 127
  128. 128
  129. 129
  130. 130
  131. 131
  132. 132
  133. 133
  134. 134
  135. 135
  136. 136
  137. 137
  138. 138
  139. 139
  140. 140
  141. 141
  142. 142
  143. 143
  144. 144
  145. 145
  146. 146
  147. 147
  148. 148
  149. 149
  150. 150

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 144 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Addu'ar Neman Ceto da Wadata

1. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, mai kiyaye ni,Ya hore ni don yaƙi,Ya kuwa shirya ni don yaƙi.

2. Shi yake kiyaye ni,Shi yake kāre ni,Shi ne mafakata da Mai Cetona,Wanda nake dogara gare shiDon samun zaman lafiya.Shi ne ya ɗora ni a kan al'ummai.

3. Ya Ubangiji wane ne mutum, har da kake lura da shi?Wane ne ɗan adam kurum, har da kake kulawa da shi?

4. Shi kamar hucin iska yake,Kwanakinsa kuwa kamar inuwa mai wucewa ne.

5. Ya Ubangiji, ka kware sararin sama, ka sauko,Ka taɓa duwatsu, don su tuƙaƙo da hayaƙi.

6. Ka aiko da walƙiyar tsawa ta warwatsa maƙiyanka,Ka harba kibanka, ka sa su sheƙa a guje!

7. Ka sunkuyo daga Sama,Ka tsamo ni daga cikin ruwa mai zurfi, ka cece ni,Ka cece ni daga ikon baƙi,

8. Waɗanda ba su taɓa faɗar gaskiya ba,Sukan yi rantsuwar ƙarya.

9. Zan raira maka sabuwar waƙa, ya Allah,Zan kaɗa garaya in raira maka waƙa.

10. Ka ba sarakuna nasara,Ka kuma ceci bawanka Dawuda.

11. Ka cece ni daga mugayen abokan gābana,Ka ƙwato ni daga ikon baƙi,Waɗanda ba su taɓa faɗar gaskiya ba,Sukan yi rantsuwar ƙarya.

12. Ka sa 'ya'yanmu maza waɗanda suke cikin samartaka,Su zama kamar itatuwan da yake girma da ƙarfi.Ka sa 'ya'yanmu mataSu zama kamar al'amudai,Waɗanda suke adanta kusurwoyin fāda.

13. Ka sa rumbunanmu su cikaDa kowane irin amfanin gona.Ka sa tumakin da suke cikin saurukanmuSu hayayyafa dubu dubu har sau goma,

14. Ka sa shanunmu su hayayyafa,Kada su yi ɓari ko su ɓace.Ka sa kada a ji kukan damuwa a kan titunanmu!

15. Mai farin ciki ce al'ummarDa abin nan da aka faɗa ya zama gaskiya a gare ta.Masu farin ciki ne jama'ar da Allahnsu shi ne Ubangiji!