Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Wajibin Mai Tsaro [Eze 3.16-21]

1. Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2. “Ɗan mutum, ka yi magana da mutanenka, ka faɗa musu cewa, ‘Idan na zare takobi a kan wata ƙasa, idan mutanen ƙasar suka ɗauki wani mutum daga cikinsu, suka sa shi ya zama ɗan tsaronsu,

3. idan ya ga an taso wa ƙasar da takobi, sai ya busa ƙaho don ya faɗakar da jama'ar.

4. Idan wani ya ji amon ƙahon, amma bai kula ba, har takobin ya zo ya kashe shi, hakkin jininsa yana bisa kansa.

5. Gama ya ji amon ƙahon, bai kuwa kula ba, hakkin jininsa zai zauna a bisa kansa. Amma idan ya kula da faɗakar, zai tsira da ransa.

6. Idan kuwa ɗan tsaron ya ga takobi yana zuwa, amma bai busa ƙahon don ya faɗakar da mutanen ba, takobin kuwa ya zo, ya kashe wani daga cikinsu, shi wanda aka kashe ya mutu saboda laifinsa, amma zan nemi hakkin jininsa daga hannun ɗan tsaron.’

7. “Yanzu fa, kai ɗan mutum, na sa ka zama ɗan tsaro a al'ummar Isra'ila. Duk lokacin da ka ji magana daga bakina, sai ka faɗakar da su.

8. Idan na hurta, cewa hakika mugu zai mutu, amma ba ka faɗakar da shi don ya juyo, ya bar muguwar hanyarsa ba, wannan mugun zai mutu saboda laifinsa, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka.

9. Amma idan ka faɗakar da mugu don ya juyo, ya bar muguwar hanyarsa, idan bai juyo ya bar muguwar hanyarsa ba, zai mutu saboda laifinsa, amma za ka tsira da ranka.”

Ayyukan Allah Daidai Ne [Eze 18.21-32]

10. “Kai ɗan mutum, sai ka faɗa wa mutanen Isra'ila, ‘Kuna cewa, “Laifofinmu da zunubanmu suna nawaita mana, muna kuwa lalacewa, yanzu fa, ta ƙaƙa za mu rayu?” ’

11. Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo, ku juyo daga mugayen hanyoyinku, gama don me za ku mutu, ya mutanen Isra'ila?’

12. “Ɗan mutum, sai kuma ka faɗa wa mutanenka, cewa adalcin adali ba zai cece shi ba sa'ad da ya yi laifi, muguntar mugu kuma ba za ta sa ya mutu ba idan ya bar muguntarsa. Adalcin adali ba zai cece shi ba, idan ya shiga aikata zunubi.

13. Idan na ce wa adali, ba shakka zai rayu, amma idan ya dogara ga adalcin da ya riga ya yi, sa'an nan ya shiga aikata laifi, ba za a tuna da ayyukan adalcinsa na dā ba. Zai mutu saboda laifin da ya yi.

14. Idan kuma na ce wa mugu ba shakka zai mutu, amma idan ya bar laifinsa, ya shiga aikata adalci,

15. idan kuma ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya ƙwace, sa'an nan ya kiyaye dokokin rai, ya daina yin laifi, hakika, zai rayu, ba zai mutu ba.

16. Ba za a tuna da laifofin da ya aikata a dā ba, gama ya aikata adalci da gaskiya, zai rayu.

17. “Amma mutanenka sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce,’ alhali kuwa tasu ce ba daidai ba.

18. Sa'ad da adali ya daina aikata adalci, ya shiga aikata laifi, zai mutu saboda laifinsa.

19. Sa'ad da kuma mugu ya daina aikata mugunta, ya shiga aikata adalci da gaskiya, zai rayu saboda adalcinsa.

20. Amma duk da haka kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ya mutanen Isra'ila, zan hukunta kowane ɗayanku gwargwadon ayyukansa.”

Labarin Faɗuwar Urushalima

21. A rana ta biyar ga watan goma, a shekara ta goma sha biyu ta zaman bautar talala da aka kai mu, sai wani ɗan gudun hijira daga Urushalima ya zo wurina, ya ce, “Birnin ya fāɗi.”

22. A maraicen da ya wuce kafin ɗan gudun hijirar ya iso, Ubangiji ya ƙarfafa ni, ya kuma buɗe bakina a lokacin da mutum ya zo wurina da safe. Bakina kuwa ya buɗe, ban zama bebe ba kuma.

23. Ubangiji kuma ya yi magana da ni, ya ce,

24. “Ɗan mutum, mazaunan wuraren nan da aka lalatar a ƙasar Isra'ila, suna cewa, ‘Ibrahim shi kaɗai ne, duk da haka an ba shi ƙasar duka, balle fa mu da muke da yawa, lalle ƙasar tamu ce.’

25. “Domin haka, sai ka faɗa musu, ‘Ubangiji Allah ya ce, “Kuna cin nama da jininsa, kuna bautar gumaka, kuna kuma yin kisankai, da haka za ku mallaki ƙasar?

26. Kun sa dogararku ga takobi kuna aikata abubuwan bankyama, kowannenku kuma yana zina da matar maƙwabcinsa, da haka za ku iya mallakar ƙasar?”’

27. “Ka faɗa musu, ‘Ubangiji ya ce, “Hakika, waɗanda suke a wuraren da aka lalatar, za a kashe su da takobi, wanda kuma yake a saura zan sa namomin jeji su cinye shi. Waɗanda kuma suke cikin kagara, da kogwannin duwatsu, annoba za ta kashe su.

28. Zan mai da ƙasar kufai marar amfani, fariya za ta ƙare. Tuddan Isra'ila za su zama kufai, ba wanda zai ratsa ta cikinsu.

29. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji, sa'ad da na mai da ƙasar kufai marar amfani saboda dukan ayyukansu na banƙyama.” ’ ”

Sakamakon Wa'azin Annabin

30. Ubangiji ya ce, “Ɗan mutum, mutanenka sun taru a kan garu da cikin ƙofofin gidaje, suna magana da juna a kanka cewa, ‘Ku zo mu tafi mu ji maganar da ta zo daga wurin Ubangiji.’

31. Sukan zo wurinka su zauna, sai ka ce su mutanena ne, sukan ji abin da ka ce, amma ba za su aikata ba, gama suna nuna ƙauna da baka, amma sun ƙwallafa zuciyarsu a kan ƙazamar riba.

32. A gare su ka zama gwanin kiɗa da waƙa, gama suna so su ji abin da kake faɗa, amma ba za su aikata ba.

33. Sa'ad da abin da kake faɗa ya cika [ba shakka kuwa zai cika], sa'an nan za su sani akwai annabi a tsakiyarsu.”