Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Annabci a kan Dutsen Seyir

1. Ubangiji ya kuma yi magana da ni, ya ce,

2. “Ɗan mutum, ka fuskanci Dutsen Seyir, ka yi annabci a kansa.

3. Ka faɗa masa, ni Ubangiji Allah na ce,Ga shi, ina gāba da shi, wato Dutsen Seyir.Zan miƙa hannuna gāba da shi,Zan maishe shi kufai, in lalatar da shi.

4. Zan lalatar da biranensa,In maishe su kufai marar amfani,Sa'an nan zai sani ni ne Ubangiji.

5. “Saboda ya riƙe ƙiyayya din din din, ya ba da mutanen Isra'ila domin a kashe su da takobi a lokacin masifarsu, da lokacin da adadin horonsu ya cika,

6. don haka, ni Ubangiji na ce, hakika zan sa a zub da jininsa. Mai zub da jini zai fafare shi, da yake shi ma ya zub da jini, domin haka mai zub da jini zai fafare shi.

7. Zan mai da Dutsen Seyir kufai marar amfani. Zan kashe duk mai shiga ko mai fita a cikinsa.

8. Zan cika duwatsunsa da gawawwaki. Waɗanda za a kashe da takobi za su faɗi a kan tuddansa, da cikin kwarurukansa, da cikin dukan kwazazzabansa.

9. Zan maishe shi kufai marar amfani har abada. Ba wanda zai zauna a cikin biranensa. Sa'an nan zai sani ni ne Ubangiji.

10. “Da yake ya ce al'umman nan biyu, da ƙasashen nan biyu za su zama nasa, ya mallake su, ko da yake Ubangiji yana cikinsu,

11. domin haka, ni Ubangiji Allah na ce, hakika zan saka masa gwargwadon fushinsa, da kishinsa, da ƙiyayyar da ya nuna musu. Zan sanar da kaina a gare su sa'ad da na hukunta shi.

12. Zai sani Ubangiji ne wanda ya ji dukan zarge zargen da ya yi wa duwatsun Isra'ila, da ya ce, ‘An maishe su kufai marar amfani, an ba mu su mu cinye!’

13. Na ji tsiwa da dukan surutan da ya yi mini.

14. “Ni Ubangiji Allah zan maishe shi kufai marar amfani, domin dukan duniya ta yi farin ciki.

15. Kamar yadda ya yi farin ciki saboda gādon jama'ar Isra'ila, da ya zama kufai marar amfani, haka nan zan yi da shi, wato Seyir. Zai zama kufai marar amfani, wato Dutsen Seyir da dukan Edom. Sa'an nan mutane za su sani ni ne Ubangiji!”