Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Annabci a kan Gog

1. Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2. “Ɗan mutum, ka fuskanci Gog na ƙasar Magog, babban shugaban Rosh, da Meshek, da Tubal, ka yi annabci a kansa,

3. ka ce Ubangiji Allah ya ce, ‘Ga shi, ina gaba da kai, ya Gog, babban shugaban Rosh, da Meshek, da Tubal.

4. Zan juyar da kai, in sa ƙugiyoyi cikin muƙamuƙanka, in fitar da kai, da dukan sojojinka, da dawakai da mahayansu. Su babbar runduna ce saye da makamai, wato garkuwoyi, da takuba a zāre,

5. mutanen Farisa, da Habasha, duk da Fut. Dukansu suna saye da garkuwa da kwalkwali,

6. da Gomer tare da dukan sojojinsa, da Bet-togarma daga ƙurewar arewa, da dukan sojojinsa, su jama'a mai yawa, suna tare da kai.

7. Ka shirya, ka kuma zama da shiri, kai da dukan rundunar da suka tattaru kewaye da kai, ka zama ɗan tsaronsu.

8. Bayan kwanaki masu yawa zan ziyarce ka, a cikar waɗannan shekaru, za ka koma ƙasar duwatsun Isra'ila, wadda ta farfaɗo daga masifar yaƙin da ta sha, ƙasa inda jama'a suka tattaru daga sauran al'umma masu yawa, wadda a dā ta yi ta lalacewa, sai da aka fito da mutanenta daga cikin al'ummai, yanzu kuwa dukansu suna zaman lafiya.

9. Za ka ci gaba, kana zuwa kamar hadiri, za ka rufe ƙasar kamar gizagizai, kai da rundunarka, da jama'a masu yawa tare da kai.”’

10. Ubangiji Allah ya ce, “A wannan rana tunani zai shiga cikin zuciyarka, za ka ƙirƙiro muguwar dabara,

11. ka ce, ‘Zan haura, in tafi ƙasar da garuruwanta ba su da garu, in fāɗa wa mutanen da suke zama cikin salama, dukansu kuwa suna zaman lafiya, garuruwansu ba garu, ba su da ko ƙyamare,

12. don in washe su ganima, in fāda wa wuraren da aka ɓarnatar waɗanda ake zaune a cikinsu yanzu, in kuma fāɗa wa jama'ar da aka tattaro daga cikin al'ummai waɗanda suka sami shanu da dukiya, suna zaune a cibiyar duniya.’

13. Sheba da Dedan, da 'yan kasuwar Tarshish, da dukan garuruwa za su ce maka, ‘Ka zo kwasar ganima ne? Ko ka zo ka tattaro rundunarka don ka yi waso, ka kwashe azurfa da zinariya, da bisashe, da dukiya, ka kwashe babbar ganima?’

14. “Saboda haka ɗan mutum, yi annabci, ka faɗa wa Gog, cewa ni Ubangiji Allah na ce, ‘A wannan rana sa'ad da jama'ata Isra'ila suna zaman lafiya, ba za ka sani ba?

15. Za ka taso daga wurin da kake, can ƙurewar arewa, da jama'a mai yawa tare da kai, babbar rundunar mayaƙa mai ƙarfi, dukansu a kan dawakai.

16. Za ka zo ka yi yaƙi da mutanen Isra'ila, za ka rufe su kamar yadda girgije yakan rufe sararin sama. A kwanaki na ƙarshe zan kawo ka ka yi yaƙi da ƙasata domin al'ummai su san ni sa'ad da na bayyana tsarkina a gabansu ta wurin abin da ka yi.”’

17. Ubangiji Allah ya ce, “Kai ne wanda na yi magana a kanka a zamanin dā ta wurin bayina annabawan Isra'ila, cewa a shekaru masu zuwa zan kawo ka, ka yaƙe su.

18. Amma a wannan rana sa'ad da Gog zai kawo wa ƙasar Isra'ila yaƙi, ni Ubangiji Allah zan hasala.

19. Gama a kishina da zafin hasalata na hurta, cewa a wannan rana za a yi babbar girgiza a ƙasar Isra'ila.

20. Kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da bisashe, da dukan masu rarrafe, da dukan mutanen da suke duniya, za su yi makyarkyata a gabana. Za a jefar da duwatsu ƙasa, tsaunuka za su fādi, kowane bango zai rushe.

21. Zan razana Gog da kowace irin razana, ni Ubangiji Allah na faɗa. Mutanensa za su sassare junansu da takubansu.

22. Zan hukunta shi da annoba da kuma zub da jini. Zan yi masa ruwa da ƙanƙara, da wuta, da kibritu za a makaka a kansa da rundunarsa, da dukan jama'ar da suke tare da shi.

23. Da haka kuwa zan bayyana girmana da tsarkina in kuma sanar da kaina ga al'ummai. Ta haka za su sani ni ne Ubangiji.”