Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Annabci a kan Taya

1. A rana ta fari ga watan, a shekara ta goma sha ɗaya, sai kuma Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,

2. “Ɗan mutum, da yake Taya ta yi magana a kan Urushalima ta ce, ‘Madalla, Urushalima ta rushe, ƙofa ta buɗu, yanzu zan wadata da yake ta zama kufai,’

3. domin haka ni, Ubangiji Allah na ce, ‘Ina gāba da ke, ke Taya, zan kawo al'ummai da yawa su yi gāba da ke, kamar yadda teku takan kawo raƙuman ruwa.

4. Za su hallaka garun Taya, su rurrushe hasumiyarta. Zan ƙan'kare ƙasarta, in maishe ta fā.

5. Za ta zama wurin shanya taruna a tsakiyar teku. Za ta kuma zama ganima ga sauran al'umma. Ni Ubangiji na faɗa.

6. Ya'yanta mata waɗanda suke zaune a filin kasar za a kashe su da takobi, sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.’ ”

7. Gama Ubangiji Allah ya ce, “Zan kawo wa Taya Nebukadnezzar, Sarkin Babila, sarkin sarakuna, daga arewa. Zai zo da dawakai da karusai, da sojojin dawakai, da babbar rundunar sojoji.

8. Zai kashe ya'yanki mata waɗanda suke a filin ƙasar da takobi. Zai kuma kewaye ki da garun yaƙi, ya gina miki mahaurai, sa'an nan zai rufe ki da garkuwoyi.

9. Zai rushe garunki da dundurusai, ya rushe hasumiyarki da gatura.

10. Saboda yawan dawakansa, ƙurar da za su tayar za ta rufe ki. Garunki kuma zai girgiza saboda motsin sojojin doki, da na ƙafafu kamar na keke, da na karusai sa'ad da ya shiga ƙofofinki, kamar yadda akan shiga birnin da garunsa ya rushe.

11. Kofatan dawakansa za su tattake dukan titunanki, zai kashe mutanenki da takobi. Manyan ginshiƙanki za su rushe.

12. Za su washe dukiyarki da kayan cinikinki. Za su kuma rurrushe garunki da kyawawan gidajenki. Za su kwashe duwatsu, da katakai, da tarkace, su zubar a cikin teku.

13. Zan sa a daina raira waƙoƙi da kaɗa garayu.

14. Zan maishe ki fā, wato wurin shanya taruna. Ba za a sāke gina ki ba, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

15. Ubangiji Allah ya ce wa Taya, “Sa'ad da kika fāɗi, ƙasashen da suke a gāɓar teku za su girgiza saboda amon fāɗuwarki, da nishin waɗanda ake yi wa rauni, da kashe-kashen da aka yi a cikinki.

16. Sa'an nan sarakunan bakin teku za su sauka daga gadajen sarautarsu, su tuɓe rigunansu, da rigunansu waɗanda aka yi wa ado. Za su zauna a ƙasa suna rawar jiki a kowane lokaci. Za su razana saboda abin da ya same ki.

17. Za su yi makoki saboda ke, su ce,‘Ke wadda ake zaune cikinki, kin bace daga tekuna,Ya shahararren birni, wanda yake babba a bakin teku,Ke da mazaunan da suke cikinki, kun sa mazaunan gāɓar teku su ji tsoro!

18. Yanzu tsibiran za su yi rawar jiki a ranar faɗuwarki.Ji, tsibiran teku za su gigice saboda shuɗewarki.’ ”

19. Gama Ubangiji Allah ya ce, “Sa'ad da na maishe ki kufai kamar biranen da ba a zauna cikinsu ba, sa'ad da kuma na dulmuye ki cikin zurfin teku,

20. sa'an nan zan tura ki tare da waɗanda suke gangarawa zuwa lahira, zuwa wurin mutanen dā. Zan sa ki zauna a ƙarƙashin ƙasa inda ya zama kufai, tare da waɗanda suke gangarawa zuwa lahira, don kada a zauna a cikinki, amma zan ƙawata ƙasar masu rai.

21. Zan sa ki yi mummunan ƙarshe, ba za ki ƙara kasancewa ba. Za a neme ki, amma ba za a same ki ba, ni Ubangiji Allah na faɗa!”