Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Ezekiyel ya Aske Kansa

1. Ubangiji ya ce, “Ya kai ɗan mutum, sai ka ɗauki takobi mai kaifi, ka more shi kamar askar wanzami, ka aske kanka da gemunka. Ka auna gashin da ma'auni, don ka raba shi kashi uku.

2. Sai ka ƙone kashi ɗaya da wuta a tsakiyar birnin sa'ad da kwanakin kewaye birnin da yaƙi suka cika. Ka kuma ɗauki sulusi ɗaya ka yanyanka da takobi kewaye da birnin. Sulusi ɗayan kuwa za ka watsar ya bi iska. Ni kuwa zan zare takobi a kansu.

3. Za ka ɗibi gashi kaɗan ka ɗaure a shafin rigarka.

4. Daga cikin gashi kaɗan ɗin nan kuma, sai ka ɗibi waɗansu ka sa a wuta. Daga nan ne wuta za ta tashi a Isra'ila duka.”

5. Ubangiji Allah ya ce, “Wannan ita ce Urushalima. Na kafa ta a tsakiyar al'ummai da ƙasashe kewaye da ita.

6. Ga shi, ta tayar wa ka'idodina da muguwar tayarwa fiye da al'ummai, ta kuma tayar wa dokokina fiye da sauran ƙasashen da suke kewaye da ita. Ta ƙi bin ka'idodina, ta kuma ƙi ta yi tafiya bisa ga dokokina.

7. Domin haka ni na ce, ‘Da yake kin cika rikici fiye da sauran ƙasashen da suke kewaye da suke, kin ƙi yin tafiya cikin dokokina, ba ki kiyaye ka'idodin ba, amma kin bi ka'ikodin al'umman da take kewaye da ke,

8. to, ina gāba da ke, zan hukunta ki a idanun al'ummai.

9. Saboda yawan abubuwa masu banƙyama da kika aikata, zan yi miki abin da ban taɓa yi ba, ba kuwa zan sāke yin irinsa ba.

10. Ubanni za su cinye 'ya'yansu, 'ya'ya kuma za su cinye ubanninsu. Zan hukunta ki, waɗanda kuma suka tsira zan watsar da su ko'ina.

11. “‘Tun da yake kin ƙazantar da Haikalina mai tsarki da gumakanki da abubuwanki masu banƙyama, hakika, ni Ubangiji Allah, zan kawar da ke, ba zan ji tausayinki ba, ba kuwa zan haƙura ba.

12. Sulusinki zai mutu da annoba da yunwa. Takobi kuma zai kashe sulusinki, sa'an nan zan watsar da sulusinki ko'ina, zan kuma zare takobi a kansu.

13. “‘Ta haka zan sa fushina ya huce, hasalata kuma a kansu ta lafa, ni kuma in wartsake. Sa'an nan za su sani ni Ubangiji na yi magana da zafin kishi sa'ad da na iyar da fushina a kansu.

14. Zan kuma maishe ki kufai da abin zargi ga al'ummai da suke kewaye da ke, da kuma a idanun dukan masu wucewa.

15. “‘Za ki zama abin zargi, da abin ba'a, da abin faɗaka, da abin tsoro ga al'ummai da suke kewaye da ke sa'ad da na hukunta ki da zarin fushina, ni Ubangiji na faɗa.

16. Gama zan aiko miki da masifu na yunwa domin hallakarwa. Zan aiko miki da su don su hallaka ki. Zan kawo miki yunwa mai tsanani, in sa abincinki ya ƙare.

17. Zan aiko miki da yunwa da namomin jeji, za su washe 'ya'yanki. Annoba da zub da jini za su ratsa cikinki. Zan kuma kawo takobi a kanki, ni Ubangiji na faɗa.”’