Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Makoki a kan Hakiman Isra'ila

1. “Sai ka yi makoki domin hakiman Isra'ila,

2. Ka ce, ‘Mahaifiyarka zakanya ce a cikin zakoki,Ta yi zamanta tare da 'yan zakoki,Ta yi renon kwiyakwiyanta.

3. Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta,Ya zama sagari,Sai ya koyi kamun nama, ya cinye mutane.

4. Da al'ummai suka ji labarinsa,Sai suka kama shi cikin wushefensu,Suka ja shi da ƙugiyoyi zuwa Masar.

5. Sa'ad da ta ga wanda ta sa zuciya a kansa ya tafi,Sai ta ɗauki ɗaya kuma daga cikin kwiyakwiyanta,Ta goye shi ya zama sagari.

6. Sai ya yi ta kai da kawowa a cikin zakoki,Ya zama sagari,Ya koyi kamun nama, ya cinye mutane.

7. Ya lalatar da kagaransu,Ya mai da biranensu kufai,Ƙasar da waɗanda suke cikinta suka tsorata da jin rurinsa.

8. Sai al'ummai suka kafa masa tarko a kowane waje,Sun kafa masa tarko,Suka kama shi cikin wushefensu.

9. Suka sa masa ƙugiyoyi, sa'an nan suka sa shi cikin suru,Suka kai shi wurin Sarkin Babila.Suka sa shi a kurkuku don kada a ƙara jin rurinsa a kan duwatsun Isra'ila.’ ”

Busasshiyar Kurangar Inabi

10. “ ‘Mahaifiyarka tana kama da kurangar inabi,Wadda aka dasa kusa da ruwa,Ta ba da 'ya'ya da rassa da yawa, saboda isasshen ruwa.

11. Rassanta masu ƙarfi sun zama sandunan masu mulki,Ta yi tsayi zuwa sama duk da rassan,Ana hangenta daga nesa.

12. Amma aka tumɓuke kurangar inabin da fushi,Aka jefar da ita ƙasa.Iskar gabas ta busar da ita,'Ya'yanta suka kakkaɓe,Rassanta masu ƙarfi sun bushe, wuta kuwa ta cinye su.

13. Yanzu na dasa ta a jeji, cikin busasshiyar ƙasa,

14. Wuta ta fito daga jikintaTa cinye rassanta da 'ya'yanta,Don haka ba wani reshe mai ƙarfi da ya ragu, wanda zai zama sandan mulki.Wannan makoki ne, ya kuwa tabbata makoki.’ ”