Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai ya ce mini, “Ɗan mutum ka ci abin da aka ba ka. Ka ci wannan littafi, sa'an nan ka tafi ka yi wa mutanen Isra'ila magana.”

2. Sai na buɗe bakina, sa'an nan ya ba ni littafin in ci.

3. Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ci littafin nan da na ba ka, ka cika tumbinka da shi.” Sai na ci littafin, na ji shi a bakina da zaƙi kamar zuma.

4. Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum ka tafi wurin mutanen Isra'ila ka faɗa musu maganata.

5. Gama ba a aike ka a wurin mutane waɗanda suke da baƙon harshe wanda ba ka sani ba, amma zuwa mutanen Isra'ila,

6. ba wurin waɗansu mutane dabam waɗanda suke da baƙon harshe mai wuya ba, wato harshen da ba ka sani ba. Da na aike ka wurin irin mutanen nan da za su ji.

7. Amma mutanen Isra'ila ba za su ji ka ba, ba su kuwa da nufi su ji ni, gama suna da taurinkai da taurin zuciya.

8. Ga shi, na sa fuskarka da goshinka su zama da tauri kamar nasu.

9. Kamar yadda lu'ulu'u ya fi ƙanƙarar dutse ƙarfi, haka nan na sa goshinka ya zama. Kada ka ji tsoronsu, ko kuwa ka karai saboda irin kallon da za su yi maka, gama su 'yan tawaye ne.”

10. Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, sai ka ji, ka karɓi dukan maganata da zan faɗa maka.

11. Sa'an nan ka tafi wurin mutanenka waɗanda suke cikin bautar talala, ka faɗa musu, ko su ji, ko kada su ji.”

12. Sa'an nan Ruhu ya ɗaga ni, sai na ji murya a bayana, kamar babban motsi, tana cewa, “Yabo ga ɗaukakar Ubangiji a kursiyinsa.”

13. Na kuma ji amon fikafikan talikan ne sa'ad da suka taɓa junansu, da kuma amon ƙafafun da suke kusa da talikan, da amon babban motsi.

14. Sai Ruhu ya ɗaga ni, ya kuma tafi da ni, na kuwa tafi da baƙin ciki, ina jin zafi a ruhuna. Ikon Ubangiji yana tare da ni da ƙarfi.

15. Na zo wurin 'yan bautar talala a Telabib, waɗanda suke bakin kogin Kebar. Na zauna tare da su kwana bakwai, ina ta mamaki.

Ezekiyel Ya Zama Mai Tsaron Isra'ila

16. A ƙarshen kwana bakwai ɗin, sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

17. “Ɗan mutum, na maishe ka mai tsaron gidan Isra'ila. Sa'ad da ka ji magana daga bakina, sai ka faɗakar da su a madadina.

18. Idan na ce wa mugu, ‘Lalle za ka mutu,’ kai kuwa ba ka faɗakar da shi a kan mugayen ayyukansa don ka ceci ransa ba, wannan mugun mutum zai mutu cikin zunubinsa, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka.

19. Amma idan ka faɗakar da mugu, ya kuwa ƙi barin muguntarsa, zai mutu cikin zunubinsa, kai kam ka kuɓuta.

20. “Idan kuma adali ya bar adalci sa'an nan ya aikata zunubi, ni kuwa na sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Zai mutu saboda zunubinsa domin ba ka faɗakar da shi ba. Ba za a tuna da ayyukansa na adalci waɗanda ya yi ba, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka.

21. Amma idan ka faɗakar da adali, kada ya aikata zunubi, shi kuwa bai aikata zunubi ba, hakika zai rayu domin ya ji faɗakar, kai kuma ka kuɓuta.”

Annabi Ya Zama Bebe

22. Ikon Ubangiji yana tare da ni, Ubangiji kuwa ya ce mini, “Tashi, ka tafi ka tsaya a fili, a can zan yi magana da kai.”

23. Sai na tashi na tafi na tsaya a fili, sai ga ɗaukakar Ubangiji a wurin, a tsaye kamar ɗaukakar da na gani a bakin kogin Kebar. Sai na fāɗi rubda ciki.

24. Ruhu kuwa ya sauko a kaina, ya ta da ni tsaye. Sai ya yi magana da ni, ya ce, “Ka tafi, ka kulle kanka cikin gida.

25. Ya ɗan mutum, za a ɗaure ka da igiyoyi don kada ka tafi cikin jama'a.

26. Ni kuwa zan sa harshenka ya manne wa dasashinka don ka zama bebe, ka kasa tsauta musu, gama su 'yan tawaye ne.

27. Amma sa'ad da na yi magana da kai, zan buɗe bakinka, kai kuwa za ka yi musu magana, ka ce, ‘Ubangiji ya ce, wanda zai ji, to, ya ji, wanda kuma zai ƙi ji, ya ƙi ji,’ gama su 'yan tawaye ne.”