Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Wahayin Haikalin da Ezekiyel Ya Gani

1. A ranar goma ga wata na farko a shekara ta ashirin da biyar ta zamanmu a bautar talala, a shekara ta goma sha huɗu da cin birnin, ikon Ubangiji ya sauko a kaina.

2. A cikin wahayi, sai Allah ya kai ni ƙasar Isra'ila, ya zaunar da ni a kan wani dutse mai tsayi ƙwarai, inda na ga wani fasali kamar birni daura da ni.

3. Sa'ad da ya kai ni can sai ga wani mutum, kamanninsa sai ka ce tagulla, yana riƙe da igiyar rama da wani irin ƙara na awo a hannunsa, yana tsaye a bakin ƙofa.

4. Sai mutumin nan ya ce mini, “Ɗan mutum ka duba da idonka, ka ji da kunnuwanka, ka kuma mai da hankali ga dukan abin da zan nuna maka, gama saboda haka aka kawo ka nan. Sai ka sanar wa jama'ar Isra'ila abin da ka gani duka.”

5. Abin da na gani Haikali ne. Akwai katanga kewaye da filin Haikalin. Tsawon karan awon kuma da yake a hannun mutumin kamu shida ne. Sai ya auna faɗin katangar ya sami kamu shida, tsayinta kuma kamu shida.

6. Ya tafi kuma wajen ƙofar gabas ya hau matakanta, ya auna dokin ƙofar, faɗinta kamu shida ne.

7. Tsawon ɗakin 'yan tsaro kamu shida ne, faɗinsa kuma kamu shida. Kamu biyar ne yake tsakanin ɗaki da ɗaki. Dokin ƙofa kuma da yake kusa da shirayin bakin ƙofar Haikali kamu shida ne.

8. Ya kuma auna shirayin bakin ƙofar da take fuskantar Haikali, kamu shida.

9. Sa'an nan ya auna shirayin bakin ƙofar kamu takwas ne. Sai kuma ya auna ginshiƙan shirayin kamu biyu ne. Shirayin ƙofar yana fuskantar ciki.

10. Akwai ɗakuna uku na 'yan tsaro a kowane gefe na ƙofar gabas, girmansu iri ɗaya ne. Ginshiƙansu kuma girmansu ɗaya ne.

11. Ya kuma auna fāɗin bakin ƙofar, kamu goma ne, tsayin ƙofar kuwa kamu goma sha uku ne.

12. Akwai, 'yar katanga a gaban ɗakunan 'yan tsaron, faɗinta kamu ɗaya ne a kowane gefe. Girman ɗakunan 'yan tsaron kuwa kamu shida ne a kowane gefe.

13. Daga bayan rufin ɗaya ɗakin 'yan tsaro zuwa bayan ɗayan rufin ya auna filin ya sami kamu ashirin da biyar.

14. Ya yi ginshiƙai kamu sittin. Akwai ɗakuna kewaye da shirayin da yake bakin ƙofa.

15. Daga gaban ƙofar shiga, zuwa kurewar shirayi na can ciki kamu hamsin ne.

16. Akwai tagogi masu murfi da yake fuskantar ɗakunan 'yan tsaro da kuma ginshikansu waɗanda suke wajen ƙofa a kewaye, haka nan kuma shirayin. Daga ciki kuma akwai tagogi a kewaye. A kowane ginshiƙi an zana siffar itatuwan dabino.

17. Sai ya kawo ni a fili na waje, ga ɗakuna da daɓe kewaye da filin. Akwai ɗakuna talatin a gaban daɓen.

18. Daɓen ya bi ta daidai gefen ƙofofin. Wannan shi ne daɓen da yake ƙasa ƙasa.

19. Sai ya auna nisan da yake tsakanin fuskar ciki ta ƙofar da take ƙasa zuwa fuskar waje ta filin ciki, ya sami kamu ɗari wajen gabas da arewa.

20. Ya kuma auna tsayin ƙofar arewa da faɗinta wadda take fuskantar filin waje.

21. Tana da ɗakuna uku na 'yan tsaro a kowane gefe. Girman ginshiƙanta da shirayinta, daidai suke da ƙofa ta fari. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuwa kamu ashirin da biyar.

22. Girman tagoginta, da na shirayin, da na siffar itatuwan dabinon da aka zana iri ɗaya ne da na ƙofar da ta fuskanci gabas. Tana da matakai bakwai. Shirayinta yana daga can ciki.

23. Fili na ciki yana da ƙofa daura da ƙofar arewa da ta gabas. Ya auna daga ƙofa zuwa ƙofa kamu ɗari.

24. Ya kuma kai ni wajen kudu, sai kuma ga wata ƙofa. Ya auna ginshiƙanta da shirayinta. Girmansu ɗaya ne, kamar na sauran.

25. Akwai tagogi kewaye da ƙofar, da shirayinta kamar na sauran. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuwa kamu ashirin da biyar.

26. Tana da matakai bakwai. Shirayinta yana daga can ciki. An zana siffar itatuwan dabino a ginshiƙanta, ɗaya a kowane gefe.

27. Akwai wata ƙofa a kudancin fili na can ciki. Ya auna daga ƙofa zuwa ƙofa kamu ɗari.

28. Ya kuma kai ni fili na can ciki, wajen ƙofar kudu, sai ya auna ƙofar, girmanta daidai yake da na sauran.

29. Haka kuma ɗakunanta na 'yan tsaro, da ginshiƙanta, da shirayinta, girmansu ɗaya yake da na sauran. Tana da tagogi kewaye da ita da shirayinta. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kamu ashirin da biyar ni.

30. Akwai shirayi kewaye, tsawonsa kamu ashirin da biyar ne, faɗinsa kuma kamu biyar ne.

31. Shirayinta yana fuskantar filin da yake waje. An zana siffar itatuwan dabino a ginshikanta. Tana kuma da matakai takwas.

32. Sai kuma ya kai ni a fili na can ciki wajen gabas. Ya auna ƙofar, girmanta daidai yake da na sauran.

33. Haka nan kuma ɗakunanta na 'yan tsaro, da ginshiƙanta, da shirayinta, girmansu daidai yake da na sauran. Tana da tagogi kewaye da ita da shirayinta. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuma kamu ashirin da biyar.

34. Shirayinta yana fuskantar filin da yake waje. Aka zana siffar itatuwan dabino a kan ginshiƙanta a kowane gefe. Tana da matakai takwas.

35. Sa'an nan kuma ya kai ni ƙofar arewa, ya auna ta. Girmanta daidai yake da na sauran.

36. Haka kuma ɗakunanta na 'yan tsaro, da ginshiƙanta, da shirayinta. Tana da tagogi kewaye da ita da shirayinta. Tsayinta kamu hamsin ne, faɗinta kuma kamu ashirin da biyar.

37. Ginshiƙai suna fuskantar filin da yake waje. Aka zana siffar itatuwan dabino a kan ginshiƙanta a kowane gefe. Ita ma matakanta takwas ne.

38. Akwai ɗaki, wanda ƙofarsa take duban ginshiƙan gyaffan ƙofofin, a wurin ake wanke hadayar ƙonawa.

39. A shirayin ƙofar akwai tebur biyu a kowane gefe, inda ake yanka hadayar ƙonawa, da hadaya don zunubi da laifi.

40. Akwai tebur biyu a sashin waje na shirayin ƙofar arewa, akwai kuma waɗansu tebur biyu a ɗayan sashin shirayin ƙofar.

41. A gab da ƙofar akwai tebur huɗu, a waje ɗaya kuma akwai huɗu. Duka guda takwas ke nan, inda za a riƙa yanka dabbobin da za a yi hadaya da su.

42. Akwai kuma tebur huɗu da aka yi da sassaƙaƙƙun duwatsu, tsawon da faɗin kowanne kamu ɗaya da rabi rabi ne, tsayi kuwa kamu guda ne. A nan za a ajiye kayan yanka hadayar ƙonawa, da ta sadaka.

43. Aka kakkafa ƙugiyoyi kewaye da cikin ɗakin, tsawonsu taƙi-taƙi. Za a riƙa ajiye naman hadaya a kan teburorin.

44. Ya kai ni fili na can ciki, sai ga ɗakuna biyu a filin. Ɗaya yana wajen ƙofar arewa, yana fuskantar kudu. Ɗayan kuma yana wajen ƙofar kudu yana fuskantar arewa.

45. Sai ya ce mini, “Wannan ɗaki wanda yake fuskantar kudu na firistoci ne waɗanda suke lura da Haikalin.

46. Ɗakin da yake fuskantar arewa na firistoci ne waɗanda suke lura da bagade. Waɗannan su ne zuriyar Zadok waɗanda su kaɗai ne daga cikin Lawiyawa da suke da iznin kusatar Ubangiji don su yi masa hidima.”

47. Ya auna filin, tsawonsa kamu ɗari ne, faɗinsa kuma kamu ɗari, wato murabba'i ke nan. Bagade kuma yana a gaban Haikalin.

48. Ya kuma kai ni a shirayin Haikalin. Ya auna ginshiƙan shirayin, kamu biyar ne a kowane gefe. Faɗin ƙofar kuwa kamu uku ne a kowane gefe.

49. Tsawon shirayin kamu ashirin ne, faɗinsa kuwa kamu goma sha ɗaya. Akwai matakan hawa, akwai kuma ginshiƙai a kowane gefe.