Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Makoki a kan Taya

1. Sai kuma Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

2. “Ya kai ɗan mutum, ka yi makoki domin Taya.

3. Ka ce mata, ita wadda take zaune a mashigin teku, wadda take kuma kasuwar mutanen da suke bakin teku, ni Ubangiji Allah na ce,‘Ke Taya, kin ce ke kyakkyawa ce cikakkiya!

4. Teku ta kewaye kan iyakarki,Maginanki sun ƙawata ki.

5. Sun yi katakanki da itacen fir na Senir,Sun sari itacen al'ul daga Lebanon don su yi miki jigon jirgin ruwa.

6. Sun yi matuƙan jirgin ruwanki da katakon itacen oak na Bashan.Sun daɓe jirgin ruwanki da itacen kasharina na bakin tekun Kittim,Sa'an nan sun manne masa hauren giwa.

7. An yi filafilan jirgin ruwanki da lilin mai kyau, mai ado daga Masar,Don ya zama alama.An yi tutar jirgin ruwanki da shuɗi da shunayya na gaɓar tekun Elisha.

8. Mazaunan Sidon da Arwad su ne matuƙa,Masu hikima, waɗanda suke cikinki, su ne jagora.

9. Dattawan Gebal da masu hikimarta suna tare da ke,Suna tattoshe mahaɗan katakon jirginki,Dukan matuƙan jiragen ruwa sun zo wurinki don kasuwanci.

10. “ ‘Mutanen Farisa, da na Lud, da na Fut suna cikin sojojinki don su yi miki yaƙi. Sun rataya garkuwoyi, da kwalkwali a cikinki. Sun samo miki daraja.

11. Mutanen Arward sun kewaye kan garunki. Mutanen Gamad kuma suna tsaron hasumiyarki. Sun rataya garkuwoyinsu a jikin garunki. Sun ƙawata ki ƙwarai.

12. “‘Tarshish abokiyar cinikinki ce, saboda yawan dukiyarki ta sayi kayan cinikinki da azurfa, da baƙin ƙarfe, da kuza, da darma.

13. Mutanen Yawan, da na Tubal, da na Meshek, abokan kasuwancinki, sun sayi kayan cinikinki da mutane da tasoshin tagulla.

14. Mutanen Togarma kuma sun sayi kayan cinikinki da dawakai da dawakan yaƙi, da alfadarai.

15. Mutane Dedan abokan cinikinki ne. Kasashe da yawa kuma na gaɓar teku sun zama kasuwarki. Sun biya ki da hauren giwa da katakon kanya.

16. Suriya kuma abokiyar cinikinki ce saboda yawan kayan cinikinki. Sun sayi kayan cinikinki, da zumurrudu, da shunayya, da kayan ado, da lilin mai taushi, da murjani, da yakutu.

17. Mutanen Yahuza da na ƙasar Isra'ila abokan cinikinki ne. Sun sayi kayan cinikinki da alkama, da zaitun, da 'ya'yan ɓaure, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi.

18. Dimashƙu kuma ta zama abokiyar cinikinki saboda yawan kayan cinikinki da yawan dukiyarki. Ta sayi kayanki da ruwan inabin Helbon, da farin ulu.

19. Mutanen Dan, da Yawan, da ulu suka sayi kayanki, wato gyararren ƙarfe da kayan yaji.

20. Dedan ta sayi kayanki da kayan dawakai.

21. Mutanen Arabiya da shugabannin Kedar sun sayi kayanki da 'yan raguna, da raguna, da awaki.

22. 'Yan kasuwar Sheba da Ra'ama sun sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri iri, da duwatsu masu daraja iri iri, da zinariya.

23. Garuruwan Haran, da Kanne, da Aidan, da fataken Sheba, da Asshur, da Kilmad sun yi ciniki da ke.

24. Sun sayar miki da tufafi masu tsada, da na shuɗi, da masu ado, da darduma masu ƙyalƙyali da kirtani, da igiyoyi waɗanda aka tufka da kyau.

25. Jiragen ruwan Tarshish suna jigilar kayan cinikinki.Don haka kin bunƙasa,Kin ɗaukaka a tsakiyar tekuna.

26. “ ‘Matuƙanki sun kai ki cikin babbar teku,Iskar gabas ta farfasa ki a tsakiyar teku.

27. Dukiyarki, da kayan cinikinki, da hajarki,Da ma'aikatanki da masu ja miki gora,Da masu tattoshe mahaɗan katakanki,Da abokan cinikinki, da dukan sojojinki,Da dukan taron jama'ar da take tare da ke,Sun dulmuya cikin tsakiyar teku a ranar halakarki.

28. Saboda kukan masu ja miki gora, ƙasa ta girgiza.

29. “ ‘Daga cikin jiragen ruwansu dukan waɗanda suke riƙe da matuƙi za su zo.Matuƙan jiragen ruwa da masu jagora za su tsaya a gaɓar teku.

30. Za su yi kuka mai zafi dominki.Za su yi hurwa, su yi birgima cikin toka.

31. Za su aske kansu saboda ke, su sa tufafin makoki.Za su yi kuka mai zafi dominki.

32. A cikin makokinsu dominki, suna kuka, suna cewa,Wa yake kama da Taya,Ita wadda take shiru a tsakiyar teku?

33. Sa'ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi,Kin wadatar da al'ummai,Kin arzuta sarakunan duniya da yawan dukiyarki da hajarki.

34. Yanzu teku ta farfashe ki cikin zurfafa,Hajarki da dukan ma'aikatan jirgin ruwanki sun nutse tare da ke.

35. Dukan mazaunan ƙasashen gāɓar tekuSun gigice saboda masifar da ta auko miki.Dukan sarakunansu sun tsorata ƙwarai,Fuskokinsu sun yamutse.

36. 'Yan kasuwa a cikin al'ummai suna yi miki ba'a,Saboda kin zama musu barazana.Ba za ki ƙara kasancewa ba har abada.’ ”