Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Zatin Ubangiji Ya Koma Haikalin

1. Bayan haka kuma sai ya kai ni ƙofar da take fuskantar gabas.

2. Sai ga zatin Allah na Isra'ila yana tahowa daga gabas. Muryar Allah ta yi amo kamar rurin teku. Duniya kuwa ta haskaka da zatinsa.

3. Wahayin da na gani ya yi kama da wahayin da na gani lokacin da ya hallaka birnin, kamar kuma wanda na gani a bakin kogin Kebar. Sai na fāɗi rubda ciki.

4. Zatin Ubangiji ya shiga Haikalin ta ƙofar gabas.

5. Ruhu kuwa ya ɗaga ni, ya kai ni a farfajiya ta can ciki, sai ga zatin Ubangiji ya cika Haikali.

6. Sa'ad da mutumin yake tsaye kusa da ni, sai Ubangiji ya yi magana da ni daga cikin Haikalin.

7. Ya ce mini, “Ɗan mutum, wannan wuri shi ne kursiyin sarautata da kilisaina, inda zan zauna tsakiyar mutanen Isra'ila har abada. Mutanen Isra'ila da sarakunansu ba za su ƙara ɓata sunana mai tsarki ta wurin bauta wa gumaka da gina siffofin sarakunansu da suka mutu ba,

8. ko kuwa ta wurin sa dokin ƙofarsu kusa da dokin ƙofata, da kuma ta kafa madogaran ƙofarsu kusa da nawa, sai dai katangar da ta yi mana tsakani. Sun ɓata sunana mai tsarki da ayyukansu masu banƙyama, don haka na hallaka su saboda sun sa na husata.

9. Yanzu sai su zubar da gumakansu da siffofin sarakunansu nesa da ni, ni kuwa zan zauna a cikinsu har abada.

Ƙa'idodin Haikali da Bagade

10. “Kai kuwa ɗan mutum, sai ka bayyana Haikalin ga mutanen Isra'ila domin su kunyata saboda muguntarsu, ka kuma sa su auna fasalin Haikalin.

11. Idan sun ji kunyar dukan abin da suka aikata, sai ka nuna musu fasalin Haikalin, da tsarinsa, da wuraren fita, da wuraren shiga, da fasalinsa duka. Ka kuma sanashe su dukan ka'idodinsa, da dukan dokokinsa. Ka rubuta a gaban idanunsu don su kiyaye, su aikata dukan dokokinsa da dukan ka'idodinsa.

12. Wannan ita ce dokar Haikalin. Dukan filin da yake kewaye a kan dutsen, za ta zama wuri mai tsarki ƙwarai.

13. “Wannan shi ne girman bagaden bisa ga tsawon kamu. A nan kamu guda daidai yake da kamu guda da taƙi. Gindinsa kamu ɗaya ne, faɗinsa kuma kamu ɗaya, faɗin da'irarsa taƙi guda ne.

14. Tsayin bagaden zai zama kamu biyu daga gindinsa zuwa ƙaramin mahaɗinsa fāɗinsa kuma kamu ɗaya ne. Daga ƙaramin mahaɗi zuwa babban mahaɗi zai zama kamu huɗu, faɗinsa kuwa kamu ɗaya.

15. Tsayin murhun bagaden zai zama kamu huɗu. A kan murhun akwai zanko guda huɗu sun miƙe sama, tsawonsu kamu guda ne.

16. Murhun bagaden zai zama murabba'i ne, wato tsawonsa kamu goma sha biyu, faɗinsa kuma kamu goma sha biyu.

17. Mahaɗin kuma zai zama kamu goma sha huɗu, murabba'i. Faɗin da'irarsa zai zama rabin kamu, kewayen gindinsa zai zama kamu ɗaya. Matakan bagaden za su fuskanci gabas.”

18. Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ni Ubangiji Allah, na ce waɗannan su ne ka'idodin bagaden. A ranar da za a kafa shi don miƙa hadayun ƙonawa da yayyafa jini a kansa,

19. sai ka ba firistoci na zuriyar Zadok, masu yi mini hidima, bijimai na yin hadaya domin zunubi.

20. Za ka ɗibi jininsa, ka shafa shi a kan zankaye huɗu na bagaden, da kan kusurwa huɗu na mahaɗin da kan da'irarsa. Ta haka za ka tsarkake bagaden, ka yi kafara dominsa.

21. Za ka kuma ɗauki bijimi na yin hadaya domin zunubi, ka kai shi waje, a wurin da aka shirya a bayan Haikalin, ka ƙone shi.

22. A kan rana ta biyu za ka miƙa bunsuru marar lahani domin yin hadaya don zunubi, bagaden kuma zai tsarkaka, kamar yadda aka tsarkake shi da bijimin.

23. Sa'ad da ka gama tsarkake shi, sai ka miƙa bijimi da rago marar lahani.

24. Za ka kawo su a gaban Ubangiji, firistoci za su barbaɗe su da gishiri, su miƙa su hadayar ƙonawa ga Ubangiji.

25. Kowace rana za ka riƙa miƙa akuya, da bijimi, da rago, marasa lahani domin yin hadaya don zunubi, har kwana bakwai.

26. Za su yi kafara har kwana bakwai don su tsarkake bagaden, su keɓe shi.

27. Sa'ad da suka cika kwanakin nan bakwai, sa'an nan a kan rana ta takwas zuwa gaba, firistoci za su miƙa hadayun ƙonawa da na salama a kan bagaden. Ni kuwa zan karɓe ku, ni Ubangiji Allah na faɗa.”