Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Hidimar Haikali

1. Ya kuma komo da ni ƙofar waje ta Haikali wadda take wajen gabas. Ƙofar kuwa tana rufe.

2. Ubangiji ya ce mini, “Wannan ƙofa za ta kasance a rufe, ba za a buɗe ta ba, ba wanda kuma zai shiga ta cikinta, gama Ubangiji Allah na Isra'ila ya shiga ta cikinta, saboda haka za ta kasance a rufe.

3. Sai dai ɗan sarki zai zauna a cikinta ya ci abinci a gaban Ubangiji. Zai shiga ta hanyar shirayin ƙofar, ya kuma fita ta wannan shirayi.”

4. Sa'an nan ya kawo ni a gaban haikalin ta hanyar ƙofar arewa. Da na duba, na ga zatin Ubangiji cike da Haikalin, sai na faɗi rubda ciki.

5. Ubangiji kuwa ya ce mini, “Ɗan mutum, ka lura sosai, ka gani da idanunka, ka kuma ji da kunnuwanka dukan abin da zan faɗa maka a kan dukan ka'idodin Haikalin Ubangiji da dukan dokokinsa. Ka lura sosai da waɗanda aka yardar musu su shiga Haikalin, da waɗanda ba a yarda musu su shiga ba.

6. “Ka ce wa 'yan tawaye, mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Ku daina ayyukanku na banƙyama.

7. Gama kuna ƙazantar da Haikalina ta wurin shigar da baƙi marasa imani da marasa kaciya, sa'ad da kuke miƙa mini hadayu na kitse da jini. Kun ta da alkawarina da ayyukanku na banƙyama.

8. Ba ku lura da hidimomina masu tsarki ba, amma kuka sa baƙi su lura da wurina mai tsarki.”’

9. Ubangiji Allah ya ce, “Ba wani baƙo marar imani da marar kaciya, daga cikin dukan baƙin da suke cikin jama'ata Isra'ila da zai shiga wurina mai tsarki.

10. “Amma Lawiyawa waɗanda suka yi nisa da ni, suka rabu da ni, suna bin gumakansu, sa'ad da mutanen Isra'ila suka karkata, za su ɗauki alhakin muguntarsu.

11. Za su zama masu hidima a cikin wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin Haikali, suna hidima a cikin Haikalin. Za su yanka hadayar ƙonawa da ta sadaka domin mutane. Za su lura da mutanen, su yi musu hidima.

12. Da yake sun hidimta wa mutane a gaban gumakansu, suka zama sanadin mugun tuntuɓe ga mutanen Isra'ila, don haka ni Ubangiji Allah, na yi rantsuwa cewa za su karɓi hakkin muguntarsu.

13. Ba za su zo kusa da ni a matsayin firistoci don su yi mini hidima ba. Ba za su zo kusa da abubuwana masu tsarki ba, amma za su sha kunya saboda ayyukansu na banƙyama.

14. Amma duk da haka zan sa su lura da Haikalin, su yi dukan hidimomin da za a yi a cikinsa.

15. “Amma Lawiyawan da suke firistoci daga zuriyar Zadok, waɗanda suka lura da Wuri Mai Tsarki sa'ad da mutanen Isra'ila suka karkace, suka bar bina, su ne za su zo kusa da ni, su yi mini hidima, za su kusace ni domin su miƙa hadaya ta kitse da jini, ni Ubangiji Allah na faɗa.

16. Za su shiga Wuri Mai Tsarki, su kusaci teburina, su yi mini hidima, su kuma kiyaye umarnina.

17. Sa'ad da suka shiga ƙofofin fili na can ciki, sai su sa rigunan lilin, kada su sa abin da aka yi shi da ulu, sa'ad da suke hidima a ƙofofin fili na can ciki, da cikin Haikalin.

18. Za su naɗa rawunan lilin, su sa wandunan lilin. Kada su sa abin da zai sa su yi zuffa.

19. Sa'ad da suka fita zuwa filin da yake waje, wurin mutane, sai su tuɓe tufafin da suka yi hidima da su, su ajiye su a tsarkakakkun ɗakuna, sa'an nan su sa waɗansu tufafi domin kada su tsarkake mutane da tsarkakakkun tufafinsu.

20. “Ba za su aske kansu ba, ba kuma za su bar zankayensu su yi tsayi ba, sai su sausaye gashin kansu.

21. Kada firist ya sha ruwan inabi sa'ad da zai shiga fili na can ciki.

22. Ba za su auri gwauruwa ba, wato wadda mijinta ya rasu, ko sakakkiya, sai budurwa daga zuriyar Isra'ila, ko kuwa matar firist wanda ya rasu.

23. “Za su koya wa jama'ata bambancin halal da haram, su kuma nuna musu yadda za su rarrabe tsakanin tsattsarka da marar tsarki.

24. Za su zama masu raba gardama, za su yanke magana bisa ga doka. Za su kiyaye idodina bisa ga tsarinsu. Za su kuma kiyaye ranakun Asabar masu tsarki.

25. “Ba za su kusaci gawa ba, don kada su ƙazantar da kansu, amma saboda mahaifi, ko mahaifiya, ko ɗa, ko 'ya, ko 'yar'uwar da ba ta kai ga yin aure ba, ko ɗan'uwa, sa iya ƙazantar da kansu.

26. Bayan ya tsarkaka, sai ya dakata har kwana bakwai.

27. A ranar da zai shiga Wuri Mai Tsarki, can fili na ciki, domin ya yi hidima a wurin, sai ya miƙa hadayarsa don zunubi, ni Ubangiji Allah na faɗa.

28. “Ba za su sami rabon gādo ba, gama ni ne rabon gādonsu. Ba za ku ba su abin mallaka a cikin Isra'ila ba, ni ne abin mallakarsu.

29. Za su ci hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya domin laifi, kowane keɓaɓɓen abu kuma cikin Isra'ila zai zama nasu.

30. Dukan nunan fari, da kowace hadaya daga dukan hadayunku, za su zama na firistoci. Za ku ba firistoci tumun farinku don albarka ta kasance a gidajenku.

31. Firistoci ba za su ci mushen kowane irin tsuntsu ko dabba ba, ba kuma za su ci waɗanda wata dabba ta kashe ba.”