Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

An La'anci Bautar Gumaka

1. Waɗansu dattawa na Isra'ila suka zo wurina, suka zauna a gabana.

2. Sai Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

3. “Ɗan mutum, waɗannan mutane sun sa zukatansu ga bin gumaka, sun sa abin tuntuɓe a gabansu, zan fa yarda su yi tambaya a wurina?

4. “Sai ka faɗa musu, cewa Ubangiji Allah ya ce duk mutumin Isra'ila, wanda ya manne wa gumaka, ya sa abin tuntuɓe a gabansa sa'an nan kuma ya zo wurin annabi, ni Ubangiji zan sāka masa gwargwadon yawan gumakansa,

5. domin in kama zukatan mutanen Isra'ila waɗanda suka zama baƙi a gare ni, saboda gumakansu.

6. “Domin haka ka ce wa mutanen Isra'ila, ‘Ubangiji ya ce ku tuba, ku rabu da gumakanku, da abubuwanku na banƙyama.

7. “‘Gama duk wanda yake na Isra'ila da dukan baƙin da suke baƙunta cikin Isra'ila, wanda ya rabu da ni, ya manne wa gumakansa, ya sa abin tuntuɓe a gabansa, sa'an nan ya zo yana roƙona a wurin annabi, ni Ubangiji zan sāka masa.

8. Zan yi gāba da mutumin nan, zan sa ya zama abin nuni, da abin karin magana, in datse shi daga cikin mutanena, za ku kuwa sani ni ne Ubangiji.

9. “Idan aka ruɗi annabin har ya yi magana, ni Ubangiji, ni ne na rinjaye shi, zan miƙa hannuna gāba da shi, zan hallaka shi daga cikin mutanena, Isra'ila.

10. Za su ɗauki alhakin hukuncinsu, wato hukuncin annabin, da hukuncin mai yin roƙonsa duk ɗaya ne,

11. don kada mutanen Isra'ila su ƙara rabuwa da ni, ko kuma su ƙara ƙazantar da kansu ta wurin laifofinsu, amma za su zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnsu,’ ni Ubangiji Allah na faɗa.”

Hukuncin Allah a kan Urushalima

12. Ubangiji ya yi magana da ni ya ce,

13. “Ɗan mutum, sa'ad da wata ƙasa ta yi mini laifi na rashin aminci, ni kuwa na miƙa hannuna gāba da ita, na toshe hanyar abincinta, na aika mata da yunwa, na kashe mata mutum duk da dabba,

14. ko da Nuhu, da Daniyel, da Ayuba suna cikinta, rayukansu ne kaɗai za su ceta saboda adalcinsu, ni Ubangiji na faɗa.

15. “Idan na sa namomin jeji su ratsa cikin ƙasar, su lalatar da ita har ta zama kufai yadda mutum ba zai iya ratsawa ta cikinta ba saboda namomin jejin,

16. ko da mutum uku ɗin nan suna cikinta, ni Ubangiji Allah na rantse da zatina, ba za su ceci 'ya'ya mata ko 'ya'ya maza ba, su ne kaɗai za su tsira, amma ƙasa za ta zama kufai.

17. “Idan kuwa na jawo wa ƙasar takobi, na ce bari takobi ya ratse ƙasar, har na kashe mata mutum duk da dabba,

18. ko da mutum uku ɗin nan suna cikinta, ni Ubangiji Allah na rantse da zatina, ba za su ceci 'ya'ya mata ko 'ya'ya maza ba, su kaɗai za su tsira.

19. Ko kuma na aika da annoba a ƙasar, na kashe mutum duk da dabba da fushina,

20. ko da Nuhu, da Daniyel, da Ayuba suna cikinta, ni Ubangiji Allah na rantse da zatina, ba za su ceci 'ya'ya mata ko 'ya'ya maza ba, rayukansu ne kaɗai za su ceta saboda adalcinsu.

21. “Ni Ubangiji Allah na ce, ‘Balle fa sa'ad da na aika wa Urushalima da hukuntaina guda huɗu masu zafi, wato takobi, da yunwa, da mugayen namomin jeji, da annoba, don in kashe mutum duk da dabba!

22. Idan kuwa waɗansu sun wanzu daga cikinta suka fita da 'ya'yansu mata da maza zuwa wurinta, za ka ga halinsu da ayyukansu, za ka tabbata, masifar da na aukar wa Urushalima, ba kawai ba ne.

23. Bisa ga halinsu da ayyukansu za ka gane abin da na yi musu ba kawai ba ne,’ ni Ubangiji na faɗa.”