Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Babban Fari

1. Maganar da Ubangiji ya yi wa Irmiya a kan fari ke nan,

2. “Yahuza tana makoki,Ƙofofin biranenta suna lalacewa,Mutanenta suna kwance a ƙasa,suna makoki,Urushalima tana kuka da babbarmurya.

3. Manyan mutanenta sun aikibarorinsu su ɗebo ruwa.Da suka je maɓuɓɓuga, sai sukatarar ba ruwa.Sai suka koma da tulunansuhaka nan,An kunyatar da su, an ƙasƙantarda su,Suka lulluɓe kansu don kunya.

4. Saboda ƙasar ta bushe,Tun da ba a yi ruwa a kanta ba,Manoma sun sha kunya,Suka lulluɓe kansu don kunya.

5. Barewa ma a saura takan gudu,Ta bar ɗanta sabon haihuwa,Domin ba ciyawa.

6. Jakunan jeji suna tsaye a kan tuddanda ba ciyawa,Suna haki kamar diloli,Idanunsu ba su ganiDomin ba abinci.”

7. Irmiya ya ce,“Ko da yake zunubanmu su neshaidunmu,Ya Ubangiji, ka yi taimako sabodasunanka!Gama kāsawarmu ta yi yawa,Domin mun yi maka zunubi.

8. Ya kai, wanda kake begen Isra'ila,Mai Cetonta a lokacin wahala,Ƙaƙa ka zama kamar baƙo a ƙasar?Kamar matafiyi wanda ya kafaalfarwarsa a gefen hanya don yakwana, ya wuce?

9. Ƙaƙa ka zama kamar wanda bai sanabin da zai yi ba,Kamar jarumin da ya kasa yinceto?Duk da haka, ya Ubangiji, kana nana tsakiyarmu.Da sunanka ake kiranmu,Kada ka bar mu!”

10. Haka Ubangiji ya ce a kan waɗannan mutane, “Sun cika son yawaceyawace, ba su iya zama wuri ɗaya, don haka ni Ubangiji, ban yarda da su ba, zan tuna da laifofinsu in hukunta zunubansu.”

11. Sai Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu'a domin lafiyar jama'an nan.

12. Ko da sun yi azumi, ba zan ji kukansu ba, ko da sun miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta sha, ba zan karɓe su ba. Amma zan hallaka su da takobi, da yunwa, da annoba.”

13. Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, ga shi, annabawa sun faɗa musu, sun ce, ‘Ba za ku ga takobi ko yunwa ba, amma zan ba ku dawwamammiyar salama a wannan wuri.’ ”

14. Ubangiji kuwa ya ce mini, “Annabawa, annabcin ƙarya suka yi da sunana. Ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba, ban kuma yi magana da su ba. Annabcin da suke yi muku na wahayin ƙarya ne, dubar da suke yi marar amfani ce, tunaninsu ne kawai.

15. Domin haka ga abin da ni Ubangiji na ce a kan annabawan da suke yin annabci da sunana, ko da yake ban aike su ba, waɗanda suke cewa, ‘Takobi da yunwa ba za su shigo ƙasan nan ba.’ Za a hallaka su da takobi da yunwa.

16. Mutanen da suka yi wa annabci, za a jefar da su waje a kan titunan Urushalima, a karkashe su da yunwa da takobi, ba wanda zai binne su, da su, da matansu, da 'ya'yansu mata da maza. Zan sa muguntarsu ta koma kansu.

17. “Irmiya, ka faɗa wa mutanen baƙinciki da ya same ka,Ka ce, ‘Bari idanuna su yi ta zub dahawaye dare da rana,Kada su daina, saboda an bugebudurwa, 'yar jama'ata,An yi mata babban rauni da dūkamai tsanani.

18. Idan na tafi cikin saura,Sai in ga waɗanda aka kashe datakobi!Idan kuma na shiga birni,Sai in ga waɗanda suke ta fama dayunwa!Gama annabi da firist, sai harkarsusuke ta yi a ƙasar,Amma ba su san abin da suke yiba.’ ”

Mutane Sun Roƙi Ubangiji

19. “Ka ƙi Yahuza ke nan ɗungum?Ranka kuma yana jin ƙyamarSihiyona ne?Me ya sa ka buge mu, har da ba zamu iya warkewa ba?Mun zuba ido ga samun salama,amma ba wani abin alheri da yazo.Mun kuma sa zuciya ga warkewa,amma sai ga razana.

20. Mun san muguntar da muka yi, yaUbangiji,Da wadda kakanninmu suka yi,Gama mun yi maka zunubi.

21. Saboda darajar sunanka, kada kawulakanta mu,Kada kuma ka ƙasƙantar dadarajar kursiyinka,Ka tuna da alkawarin da ka yimana,Kada ka ta da shi.

22. A cikin gumakan al'ummai akwaimai iya sa a yi ruwa?Sammai kuma su yi yayyafi?Ashe, ba kai ne ba, ya UbangijiAllahnmu?Domin haka a gare ka muke sazuciya,Gama kai ne mai yin waɗannanabubuwa duka.”