Surori

 1. 1
 2. 2
 3. 3
 4. 4
 5. 5
 6. 6
 7. 7
 8. 8
 9. 9
 10. 10
 11. 11
 12. 12
 13. 13
 14. 14
 15. 15
 16. 16
 17. 17
 18. 18
 19. 19
 20. 20
 21. 21
 22. 22
 23. 23
 24. 24
 25. 25
 26. 26
 27. 27
 28. 28
 29. 29
 30. 30
 31. 31
 32. 32
 33. 33
 34. 34
 35. 35
 36. 36
 37. 37
 38. 38
 39. 39
 40. 40
 41. 41
 42. 42
 43. 43
 44. 44
 45. 45
 46. 46
 47. 47
 48. 48
 49. 49
 50. 50
 51. 51
 52. 52

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 48 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Jawabin Ubangiji a kan Mowab

1. Ga abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya faɗa a kan Mowab,“Kaiton Nebo, gama ta lalace!An kunyatar da Kiriyatayim, an ci tada yaƙi,An kunyatar da kagararta, an rusheta.

2. Darajar Mowab ta ƙare.Ana shirya mata maƙarƙashiya aHeshbon,‘Bari mu je mu ɓata ta daga zamanal'umma!’Ke kuma Madmen za ki yi shiru,Takobi zai runtume ki.

3. Muryar kuka daga Horonayim tanacewa,‘Risɓewa da babbar halaka!’

4. “An hallakar da Mowab,Ƙanananta suna kuka.

5. Gama a hawan Luhit, za su hau dakuka,Gama a gangaren Horonayim,Suna jin kukan wahalar halaka.

6. Ku gudu don ku tserar darayukanku,Ku gudu kamar jakin jeji.

7. “Kun dogara ga ƙarfinku dawadatarku,Amma yanzu za a ci ku da yaƙi,Kemosh zai tafi bautaTare da firistocinsa dashugabanninsa.

8. Mai hallakarwa zai shiga kowanegari,Don haka ba garin da zai tsira.Kwari da tudu za su lalace,Ni Ubangiji na faɗa.

9. Ku ba Mowab fikafikai,Gama za ta tashi ta gudu,Garuruwanta za su zama kango,Ba mazauna cikinsu.

10. “La'ananne ne shi wanda yake yinaikin Ubangiji da ha'inci,La'ananne ne shi kuma wanda yahana wa takobinsa jini.

11. “Tun daga ƙuruciya Mowab tanazama lami lafiya,Hankali kwance,Ba a jujjuya ta daga tulu zuwa tuluba,Ba a taɓa kai ta bauta ba,Domin haka daɗin ɗanɗanonta bairabu da ita ba,Ƙanshinta kuma bai sāke ba.”

12. Ubangiji ya ce, “Domin haka kwanaki suna zuwa, sa'ad da zai aika da mutane su tuntsurar da tuluna, su zubar da ruwan inabi, su farfasa tulunanta.

13. Sa'an nan Kemosh zai kunyatar da Mowab, kamar yadda Betel wadda Isra'ilawa suka dogara gare ta ta kunyatar da su.

14. “Don me kake cewa,‘Mu jarumawa ne, mayaƙan gaske?’

15. Mai hallaka Mowab da garuruwantaya taho,Zaɓaɓɓun majiya ƙarfinta sungangara mayanka,Ni sarki, mai suna Ubangiji MaiRunduna, na faɗa.

16. Masifar Mowab ta kusato,Halakarta kuma tana gaggabtowa.

17. “Ku yi makoki dominta, ku da kukekewaye da ita,Dukanku da kuka san sunanta, kuce,‘Ƙaƙa sandan sarauta mai ikoDa sanda mai daraja ya karye?’

18. Ku da kuke zaune a Dibon,Ku sauka daga wurin zamanku maidaraja,Ku zauna a busasshiyar ƙasa,Gama mai hallaka Mowab ya zo yayi gab da ku.Ya riga ya rushe kagararku.

19. Ku mazaunan Arower,Ku tsaya a kan hanya, ku jira,Ku tambayi wanda yake guduDa wanda yake tserewa,Abin da ya faru.

20. An kunyatar da Mowab, ta rushe.Ku yi kuka dominta,Ku faɗa a Arnon, cewa Mowab tahalaka.

21. “Hukunci ya auka kan garuruwan da suke a ƙasar fili, wato Holon, da Yahaza, da Mefayat,

22. da Dibon, da Nebo, da Bet-diblatayim,

23. da Kiriyatayim, da Bet-gamal, da Ba'almeyon,

24. da Kiriyot, da Bozara. Hukunci ya zo a kan dukan garuruwan Mowab na nesa da na kusa.

25. An karye ikon Mowab da ƙarfinta, ni Ubangiji na faɗa.

26. “Ku sa Mowab ta yi maye domin ta tayar wa Ubangiji. Za ta yi birgima cikin amanta, mutane kuwa za su yi dariya.

27. Kin yi wa mutanen Isra'ila dariya. A kowane lokacin da kika ambaci sunansu, sai ki taɗa kanki da raini kamar an kama su tare da ɓarayi.

28. “Ku mazaunan Mowab, ku bargaruruwanku,Ku tafi, ku zauna a kogwanni,Ku zama kamar kurciya wadda takeyin sheƙarta a bakin kwazazzabo.

29. Mun ji labarin girmankan Mowab,da ɗaukaka kanta,Da alfarmarta, da izgilinta,Tana da girmankai ƙwarai.

30. Ni Ubangiji na san Mowab tana dagirmankai,Alfarmarta ta banza ce,Ayyukanta kuma na banza ne.

31. Don haka zan yi kuka sabodaMowab duka,Zan kuma yi baƙin ciki sabodamutanen Kir-heres.

32. Zan yi kuka saboda kurangar inabinSibmaFiye da yadda zan yi kuka sabodamutanen Yazar.Rassanku sun haye teku har sun kaiYazar,Amma mai hallakarwa ya faɗo a kan'ya'yan itatuwanku da damunaDa kan amfanin inabinku.

33. An ɗauke farin ciki da murna dagaƙasa mai albarka ta Mowab,Na hana ruwan inabi malala dagawurin matsewarsa,Ba wanda yake matse shi, yana ihu namurna,Ihun da ake yi ba na murna ba ne.

34. “Mutanen Heshbon da na Eleyale suna kururuwa ana iya jin kururuwansu a Yahaza. Ana iya jinta kuma a Zowar, da Horonayim, da Eglat-shelishiya. Har ma ruwan Nimra ya ƙafe.

35. Zan hana mutanen Mowab miƙa hadayu na ƙonawa a tuddai, da miƙa wa gumakansu sadaka, ni Ubangiji na faɗa.

36. “Zuciyata tana makoki domin Mowab da Kir-heres kamar wanda yake kukan makoki da sarewa saboda wadatarsu ta ƙare.

37. Gama kowa ya aske kansa da gemunsa, sun tsattsage hannuwansu. Kowa kuma ya sa rigar makoki.

38. Ba abin da ake yi a bisa kan soraye da dandali na Mowab sai baƙin ciki, gama na farfashe Mowab kamar tulun da ba a so, ni Ubangiji na faɗa.

39. An farfashe Mowab, ta yi kuka, ta kunyata! Ta zama abin dariya da abin tsoro ga waɗanda suke kewaye da ita.

40. “Ni Ubangiji na ce,Wani zai yi firiya da sauri kamargaggafa,Zai shimfiɗa fikafikansa a kanMowab.

41. Za a ci garuruwa da kagarai dayaƙi,A wannan rana zukatan sojojinMowabZa su zama kamar zuciyar macen datake naƙuda.

42. Za a hallaka Mowab daga zamanal'umma,Domin ta tayar wa Ubangiji.

43. Tsoro, da rami, da tarko sunajiranku,Ya mazaunan Mowab,Ni Ubangiji na faɗa.

44. Wanda ya guje wa tsoro,Zai fāɗa a rami,Wanda kuma ya fito daga cikinrami,Tarko zai kama shi.Gama na sa wa Mowab lokacin dazan hukunta ta,Ni Ubangiji na faɗa.

45. “A ƙarƙashin inuwar Heshbon 'yangudun hijira suna tsaye ba ƙarfi.Gama wuta ta ɓullo daga Heshbon,Harshen wuta kuma ya fito dagaSihon,Ta ƙone goshin Mowab daƙoƙwan kai na 'yan tayarwa.

46. Kaitonku, ya Mowabawa!Mutanen Kemosh sun lalace,An kai 'ya'yanku mata da mazacikin bauta.

47. “Amma zan komar da mutanenMowab nan gaba,Ni Ubangiji na faɗa.”Wannan shi ne hukuncin Mowab.