Surori

 1. 1
 2. 2
 3. 3
 4. 4
 5. 5
 6. 6
 7. 7
 8. 8
 9. 9
 10. 10
 11. 11
 12. 12
 13. 13
 14. 14
 15. 15
 16. 16
 17. 17
 18. 18
 19. 19
 20. 20
 21. 21
 22. 22
 23. 23
 24. 24
 25. 25
 26. 26
 27. 27
 28. 28
 29. 29
 30. 30
 31. 31
 32. 32
 33. 33
 34. 34
 35. 35
 36. 36
 37. 37
 38. 38
 39. 39
 40. 40
 41. 41
 42. 42
 43. 43
 44. 44
 45. 45
 46. 46
 47. 47
 48. 48
 49. 49
 50. 50
 51. 51
 52. 52

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Jawabin Ubangiji a kan Filistiyawa

1. Kafin Fir'auna ya ci Gaza da yaƙi Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan Filistiyawa.

2. Ubangiji ya ce,“Ga shi, ruwa yana tasowa dagaarewa,Zai zama kogi da yake ambaliya.Zai malala bisa ƙasa da dukan abinda yake cikinta,Da birni da mazauna cikinsa,Maza za su yi kuka,Dukan mazaunan ƙasar za su yi kuka.

3. Da jin takawar kofatan dawakai,Da amon karusai da ƙafafun karusai,Ubanni ba su juya, su dubi'ya'yansu ba,Domin hannuwansu sun yi laƙwas,

4. Domin lokacin hallaka dukanFilistiyawa ya yi.Za a datse wa Taya da Sidon kowanetaimakon da ya ragu,Gama Ubangiji zai hallakaFilistiyawaWaɗanda suke baƙin teku na Kaftor.

5. Baƙin ciki zalla ya sami Gaza,Ashkelon ta lalace.Ya ƙattin mutane, yaushe za kudaina tsattsage kanku?

6. Ya takobin Ubangiji, yaushe za kahuta?Sai ka koma ƙubenka,Ka huta, ka yi shiru!

7. Ƙaƙa zai huta, tun da ni Ubangiji nena umarce shi?Ni Ubangiji na umarce shi ya yi yaƙida AshkelonDa mazauna a bakin teku.”