Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 1 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Horon Allah a kan Maƙwabtan Isra'ila

1. Ga zantuttukan Amos, ɗaya daga cikin makiyayan ƙauyen Tekowa. Allah ya bayyana wa Amos wannan saƙo, tun shekara biyu kafin girgizar duniya, a lokacin da Azariya yake sarautar Yahuza, Yerobowam ɗan Yehowash kuwa yake sarautar Isra'ila.

2. Amos ya ce,“Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona,Muryarsa za ta yi tsawa dagaUrushalima.Da jin wannan, sai wuraren kiwo zasu bushe,Ƙwanƙolin Dutsen Karmel, da yakekore zai yi yaushi.”

Suriya

3. Ubangiji ya ce,“Mutanen Dimashƙu sun ci gaba dayin zunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun zalunci mutanen Gileyad dazalunci mai tsanani.

4. Don haka zan aukar da wuta a kanfādar Sarkin Suriya.Za ta ƙone kagarar Ben-hadad,sarki.

5. Zan ragargaje ƙyamaren ƙofofinbirnin Dimashƙu,In kawar da masu sarautar Bet-edenda na kwarin Awen.Za a kwashe mutanen Suriya ganimazuwa ƙasar Kir.”

Filistiya

6. Ubangiji ya ce,“Mutanen Gaza sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun kwashe al'umma duka, sunsayar wa mutanen Edom.

7. Saboda haka zan aukar da wuta akan garun Gaza ta ƙone kagararbirnin.

8. Zan kawar da masu sarautar biranenAshdod da Ashkelon,Zan karɓe sandan mulkin Ekron.Sauran Filistiyawa da suka ragukuma,Za su mutu duka.”

Taya

9. Ubangiji ya ce,“Mutanen Taya sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun kwashe mutanen sun kaiƙasar Edom.Suka karya yarjejeniyar abuta waddasuka yi.

10. Saboda haka zan aukar da wuta akan garun Taya,Ta ƙone kagarar birnin.”

Edom

11. Ubangiji ya ce,“Mutanen Edom sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don sun farauci 'yan'uwansu,Isra'ilawa,Suka ƙi su nuna musu jinƙai.Ba su yarda su huce daga fushinsuba.

12. Saboda haka zan aukar da wuta akan Teman,Ta ƙone kagarar Bozara.”

Ammon

13. Ubangiji ya ce,“Mutanen Ammon sun ci gaba da yinzunubi.Hakika, zan hukunta su,Don haɗamarsu ta ƙasa,Suka tsaga mata masu ciki aGileyad.

14. Saboda haka zan aukar da wuta akan garun Rabba,Ta ƙone kagarar birnin.Za a yi kururuwa a ranar yaƙi,Faɗan kuwa zai yi rugugi kamarhadiri.