Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Wahayi na Huɗu, Kwandon Ɓaure na Ci

1. Ubangiji ya nuna mini wahayi, sai na ga kwandon ɓaure na ci.

2. Sai Ubangiji ya ce, “Amos, me ka gani?”Na ce, “Kwandon ɓaure na ci.”Ubangiji kuma ya ce mini, “Ƙarshen jama'ata Isra'ila ya zo. Ba zan sāke nufina a kan yi musu hukunci ba.

3. Waƙoƙin da akan raira a fāda, za su zama na makoki a wannan rana. Za a iske gawawwaki ko'ina. Ba za a ji motsin kome ba.”

An kai Ƙarshen Isra'ila

4. Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata, kuna ƙoƙari ku hallakar da matalautan ƙasar.

5. Kuna ce wa kanku, “Mun ƙosakeɓaɓɓun kwanakin nan su wuce,Mu sami damar yin kasuwancinmu.Yaushe Asabar ɗin za ta ƙare ne?Ko mā sami damar kai hatsinmukasuwa,Mu sayar musu da tsada,Mu yi awo da ma'aunin zalunci,Mu daidaita ma'auni yadda za mucuci mai saya?

6. Za mu sayi matalauci da azurfa yazama bawa,Mai fatara kuma da takalmabi-shanu.Za mu sayar da ruɓaɓɓen hatsi,Mu ci riba mai yawa.”

7. Ubangiji Allahn Isra'ila ya riga yarantse,Ya ce, “Ba zan manta da mugayenayyukanku ba.

8. Shi ya sa ƙasar za ta girgiza,Duk wanda yake cikinta zai yi baƙinciki.Ƙasa duka za ta girgiza.Za ta hau ta sauka kamar Kogin Nilu.

9. A wannan lokaci rana za ta fāɗi datsakar rana,Duniya ta duhunta da rana kata.Ni, Ubangiji ne na faɗa.

10. Zan mai da bukukuwanku makoki,In sa waƙoƙinku na murna su zamana makoki.Zan sa muku tufafin makoki,In sa ku aske kanku.Za ku yi makoki kamar iyayen dasuka rasa tilon ɗansu.Ranan nan mai ɗaci ce har ƙarshe.

11. “Lokaci yana zuwa da zan aiko dayunwa a ƙasar.Mutane za su ji yunwa,Ba ta abinci ba,Za su ji ƙishi,Ba na ruwa ba.Za su ji yunwar rashin samun saƙodaga wurin Ubangiji.Ni Ubangiji ne, na faɗa.

12. Mutane za su raunana, su riƙa kaida kawowa,Daga gabas zuwa yamma, dagakuma kudu zuwa arewa.Za su dudduba ko'ina suna nemansaƙo daga Ubangiji,Ba kuwa za su samu ba.

13. A ranan nan kyawawan 'yan matada samariZa su faɗi saboda ƙishirwa.

14. Waɗanda suka yi rantsuwa dagumakan Samariya,Waɗanda suka ce, ‘Na rantse dagunkin Dan,Da ran gunkin Biyer-sheba,’Irin waɗannan mutane za su fāɗi,Ba za su ƙara tashi ba.”