Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Ba a Kauce wa Hukuncin Allah

1. Na ga Ubangiji na tsaye a wajen bagade. Ya yi umarni, ya ce,“Bugi ginshiƙan Haikali don shirayiduka yă girgiza.Farfasa su, su fāɗi a kan mutane!Sauran mutane kuwa,Zan kashe su a wurin yaƙi.Ba wanda zai tsere, ko ɗaya.

2. Ko da za su nutsa zuwa lahira,Zan kama su.Ko sun hau Sama,Zan turo su.

3. Ko da za su hau su ɓuya a bisaƙwanƙolin Dutsen Karmel,Zan neme su in cafko su.Ko da za su ɓuya mini a ƙarƙashinteku,Sai in sa dodon ruwa yă yayyage su.

4. Idan kuwa abokan gābansu ne sukakama su,In umarce su su hallaka su datakobi,Tun da na yi ƙudurin ƙare su.”

5. Ubangiji Allah Mai RundunaYa taɓi duniya, ta girgiza.Duk waɗanda suke zaune cikintaSuna baƙin ciki.Duniya duka takan hauTa kuma gangara kamar ruwanKogin Nilu.

6. Ubangiji ya gina al'arshinsa a sama,Ya shimfiɗa samaniya a bisa duniya.Ya sa ruwan teku ya zo,Ya kwarara shi a bisa duniya.Sunansa Ubangiji ne!

7. Ubangiji ya ce, “Jama'ar Isra'ila,Ina yi da ku daidai yadda nake yi daHabashawa.Na fito da Filistiyawa daga Kaftor,Suriyawa kuwa daga Kir,Daidai yadda na fito da ku dagaMasar.

8. Ina dai kallon mulkin nan mai zunubi.Zan hallaka su daga duniya,Amma ba zan hallaka dukan jama'arYakubu ba.

9. “Zan umarta a rairayi jama'ar Isra'ilaDa matankaɗi kamar hatsi.Zan rairaye su daga cikin sauranal'umma,Duk da haka ko ƙwaya ɗaya ba zata salwanta ba.

10. Masu zunubi daga cikin jama'ata zasu mutu a yaƙi,Wato dukansu da suke cewa,‘Allah ba zai bar wata masifa takusace mu ba!’ ”

Ceton da Za a Yi wa Isra'ila Nan Gaba

11. “Wata rana zan sāke tayar da birninDawudaTankar yadda akan ta da gidan da yarushe.Zan gyara garunsa, in sāke mai dashi.Zan sāke gina shi in mai da shikamar yadda yake tun dā.

12. Ta haka jama'ar Isra'ila za ta cinasara bisa sauran ƙasar Edomwadda ta ragu,Da bisa dukan al'umman da a dā sunawa ne,”In ji Ubangiji, wanda zai saal'amarin ya auku.

13. Ubangiji ya ce, “Kwanaki sunazuwa,Sa'ad da girbi zai bi bayan huda nanda nan,Matsewar ruwan inabi kumaZa ta bi bayan shuka nan danan.Duwatsu za su zubo da ruwan inabimai zaƙi,Tuddai kuma su gudano da shi.

14. Zan komo da mutanena ƙasarsu,Za su giggina biranensu da sukarurrushe,Su zauna a cikinsu.Za su shuka gonakin inabi, su sharuwan inabin.Za su yi lambuna, su ci amfaninsu.

15. Zan dasa su a ƙasar da na ba su,Ba kuwa za a ƙara tumɓuke suba.”Ubangiji Allahnku ne ya faɗa.