Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku kasa kunne ga wannan, ya kumatan Samariya,Ku da kuka yi ƙiba kamarturkakkun shanu,Ku da kuke wulakanta kasassu,Kuna yi wa matalauta danniya,Kukan umarci mazajenku,Ku ce, “Kawo mini abin sha!”

2. Da yake Ubangiji Mai Tsarki neYa riga ya yi alkawari,Ya ce, “Hakika kwanaki za su zoDa za a jawo ku da ƙugiyoyi,Kowannenku zai zama kamar kifi aƙugiya.

3. Za a kwashe ku, a fitar da kuTa inda garu ya tsage na mafi kusaduka, a jefar.”

Isra'ila Sun Kāsa Koyo

4. Ubangiji ya ce,“Jama'ar Isra'ila,Ku tafi Betel, tsattsarkan wuri,Ku yi ta zunubi!Ku tafi Gilgal ku ƙara zunubi!Ku yi ta kawo dabbobi sadakakowace safiya.A kowace rana ta ukuKu yi ta ba da zaka.

5. Ku miƙa abincinku hadaya tagodiya.Ku yi ta yin fariya da hadayarku tayardar rai!Gama irin abin da kuke jin daɗin yike nan.”

6. Ubangiji ya ce,“Ai, ni ne, na sa a yi yunwa abiranenku.Shi ya sa ba ku da abinci.Duk da haka ba ku juyo gare ni ba.

7. Na hana wa shuke-shukenku ruwaA lokacin da suka fi bukata.Na sa a yi ruwa a wani birni,A wani birni kuwa na hana,Wata gonar ta sami ruwan sama,Amma wadda ba ta samu ba tabushe.

8. Ƙishirwa ta sa jama'a su tafke harbirane biyu ko ukuSuka tafi neman ruwa a birnin dasuke maƙwabtaka da shi,A nan ma ba su sami isasshen ruwansha ba,Duk da haka ba ku komo wurinaba.

9. “Na sa darɓa, da domanaSu lalatar da amfanin gonakinku.Fāra kuma ta cinye lambunankuDa gonakin inabinku, da itatuwanɓaurenku,Da na zaitun ɗinku.Duk da haka ba ku komo wurina ba.

10. “Na aukar muku da annoba irinwadda na aukar wa Masar.Na karkashe samarinku a wurinyaƙi,Na kwashe dawakanku.Na cika hancinku da ɗoyinsansaninku.Duk da haka ba ku komo wurina ba.

11. “Na hallakar da waɗansunkuKamar yadda na hallakar da Sadumada Gwamrata.Kamar sanda kuke, wanda aka fizgedaga wuta.Duk da haka ba ku komo wurinaba.

12. Saboda haka, jama'ar Isra'ila,Ga abin da zan yi muku,Zan kuwa yi shi duk,Sai ku yi shirin zuwa gabanUbangiji.”