Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Amos 6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Halakar Isra'ila

1. Taku ta ƙare, ku da kuke zamansakewa a Sihiyona,Da ku da kuke tsammani kunazaman lafiya a Samariya,Ku da kuke manyan mutaneNa wannan babbar al'umma taIsra'ila,Waɗanda jama'a suke zuwa a gare suneman taimako!

2. Ku je ku duba a birnin Kalne.Sa'an nan ku zarce zuwa babbanbirnin Hamat,Har zuwa birnin Gat ta Filistiyawa.Sun fi mulkin Yahuza da Isra'ila ne?Ko kuwa, yankin ƙasarsu ya finaku?

3. Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannanrana ta masifa,Amma ga shi, goyon bayan hargitsikuke ta yi,Ta wurin ayyukanku.

4. Taku ta ƙare, ku da kuke kwancekan gadajen hauren giwa,Kuna jin daɗin miƙe jiki a dogayenkujerunku,Ku ci naman maraƙi da na rago.

5. Kukan so ku tsara waƙoƙi kamaryadda Dawuda ya yi,Ku raira su da garayu.

6. Da manyan kwanoni kuke shanruwan inabi,Ku shafe jiki da mai mafi kyau,Amma ba ku yin makoki sabodalalacewar Isra'ila.

7. Don haka, ku ne na fari da za a sa suyi ƙauraBukukuwanku da shagulgulanku zasu ƙare.

8. Ubangiji kansa ne ya rantse.Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce,“Ba na son girmankai na jama'arIsra'ila.Ba na son fādodinsu.Zan ba da birnin da dukan abin dayake cikinsa ga abokan gābansu.”

9. Ko da a ce mutum goma ne suka ragu a gida guda, duk za su mutu.

10. Sa'ad da dangin mamacin ya shiga don ya fitar da gawar, ya ƙone, sai ya yi kira ga ko wane ne da yake ɓoye a gidan, ya ce, “Ko akwai wani kuma a nan?”Sai a amsa, “A'a.”Zai ce, “Kul! Kada a ambaci sunan Ubangiji.”

11. Sa'ad da Ubangiji ya ba da umarni, babban gida da ƙarami rushewa za su yi.

12. Dawakai sukan yi sukuwa aduwatsu?Ana huɗan teku da garmarshanu?Duk da haka kuka mai da adalcidafi,Kuka mai da nagarta, mugunta.

13. Kuna fariyar cin garin Lodebar, watowofi, da yaƙi.Kun ce, “Ƙarfinmu ya isa har mu ciKarnayim, wato ƙaho biyu, dayaƙi.”