Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 43:10-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. “Kai kuwa ɗan mutum, sai ka bayyana Haikalin ga mutanen Isra'ila domin su kunyata saboda muguntarsu, ka kuma sa su auna fasalin Haikalin.

11. Idan sun ji kunyar dukan abin da suka aikata, sai ka nuna musu fasalin Haikalin, da tsarinsa, da wuraren fita, da wuraren shiga, da fasalinsa duka. Ka kuma sanashe su dukan ka'idodinsa, da dukan dokokinsa. Ka rubuta a gaban idanunsu don su kiyaye, su aikata dukan dokokinsa da dukan ka'idodinsa.

12. Wannan ita ce dokar Haikalin. Dukan filin da yake kewaye a kan dutsen, za ta zama wuri mai tsarki ƙwarai.

13. “Wannan shi ne girman bagaden bisa ga tsawon kamu. A nan kamu guda daidai yake da kamu guda da taƙi. Gindinsa kamu ɗaya ne, faɗinsa kuma kamu ɗaya, faɗin da'irarsa taƙi guda ne.

14. Tsayin bagaden zai zama kamu biyu daga gindinsa zuwa ƙaramin mahaɗinsa fāɗinsa kuma kamu ɗaya ne. Daga ƙaramin mahaɗi zuwa babban mahaɗi zai zama kamu huɗu, faɗinsa kuwa kamu ɗaya.

15. Tsayin murhun bagaden zai zama kamu huɗu. A kan murhun akwai zanko guda huɗu sun miƙe sama, tsawonsu kamu guda ne.

16. Murhun bagaden zai zama murabba'i ne, wato tsawonsa kamu goma sha biyu, faɗinsa kuma kamu goma sha biyu.

17. Mahaɗin kuma zai zama kamu goma sha huɗu, murabba'i. Faɗin da'irarsa zai zama rabin kamu, kewayen gindinsa zai zama kamu ɗaya. Matakan bagaden za su fuskanci gabas.”

18. Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ni Ubangiji Allah, na ce waɗannan su ne ka'idodin bagaden. A ranar da za a kafa shi don miƙa hadayun ƙonawa da yayyafa jini a kansa,

19. sai ka ba firistoci na zuriyar Zadok, masu yi mini hidima, bijimai na yin hadaya domin zunubi.

20. Za ka ɗibi jininsa, ka shafa shi a kan zankaye huɗu na bagaden, da kan kusurwa huɗu na mahaɗin da kan da'irarsa. Ta haka za ka tsarkake bagaden, ka yi kafara dominsa.

21. Za ka kuma ɗauki bijimi na yin hadaya domin zunubi, ka kai shi waje, a wurin da aka shirya a bayan Haikalin, ka ƙone shi.

Karanta cikakken babi Ez 43