Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

An Ceci Yahuza daga Sennakerib

1. Da sai sarki Hezekiya ya ji abin da suka faɗa, sai ya kyakkece tufafinsa don baƙin ciki, ya sa tsummoki a jiki, ya shiga Haikalin Ubangiji.

2. Ya aiki Eliyakim mai kula da fāda, da Shebna marubucin ɗakin shari'a, da manyan firistoci zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz. Su kuma suna saye da tsummoki.

3. Ga saƙon da ya aike su su faɗa wa Ishaya, “Yau rana ce ta wahala, muna shan hukunci da wulakanci. Mun zama daidai da mace wadda take naƙuda, amma ba ta da ƙarfin da za ta haihu.

4. Sarkin Assuriya ya aiko babban shugaban mayaƙansa don ya zagi Allah mai rai. Da ma Ubangiji Allahnka ya ji waɗannan zage-zage ya kuma hukunta waɗanda suka yi su. Don haka sai ka yi addu'a ga Allah saboda mutanenmu waɗanda suka ragu.”

5. Sa'ad da Ishaya ya karɓi saƙon sarki Hezekiya,

6. sai ya aika masa da amsa cewa, “Ubangiji ya ce kada ka damu da irin zargin da Assuriyawa suke ta yi a kansa.

7. Ubangiji zai sa Sarkin Assuriya ya ji jita-jitar da za ta sa ya koma ƙasarsa, Ubangiji kuwa zai kashe shi a can.”

8. Shugaban mayaƙan Assuriya ya ji labari sarkin ya bar Lakish, yana can yana yaƙi da birnin Libna sai ya janye.

9. Sai Assuriyawa suka ji, cewa mayaƙan Masarawa, waɗanda sarki Tirhaka na Habasha take yi wa jagora, suna zuwa su far musu da yaƙi. Sa'ad da sarkin ya ji haka sai ya aika wa sarki Hezekiya da wasiƙa,

10. ya ce masa, “Allahn da kake dogara gare shi ya faɗa maka, ba za ka faɗa a hannuna ba, amma kada ka yarda wannan ya ruɗe ka.

11. Ka dai ji abin da Sarkin Assuriya ya yi wa duk ƙasar da ya yi niyyar hallakarwa. Kana tsammani za ka kuɓuta?

12. Kakannina sun hallakar da biranen Gozan, da Haran, da Rezef, suka kuma kashe mutanen Eden, mazaunan Telassar, ba ko ɗaya daga cikin gumakansu da ya iya cetonsu.

13. Ina sarakunan biranen Hamat da Arfad, da Sefarwayim, da Hena, da Iwwa?”

14. Sarki Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga hannun manzannin, ya karanta ta. Sa'an nan ya shiga Haikali, ya ajiye wasiƙar a gaban Ubangiji,

15. ya yi addu'a,

16. ya ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, kana kan kursiyinka, kai kaɗai ne Allah, kana mulkin dukan mulkokin duniya. Ka halicci duniya da sararin sama.

17. Yanzu, ya Ubangiji, ka ji mu, ka kuma dube mu. Ka kasa kunne ga dukan abubuwan da Senakerib yake ta faɗa, yana zaginka, ya Allah mai rai.

18. Dukanmu mun sani, ya Ubangiji, yadda sarakunan Assuriya suka hallakar da al'ummai masu yawa, suka mai da ƙasashensu kufai, marasa amfani,

19. suka ƙaƙƙone gumakansu waɗanda ba Allah ba ne ko kaɗan, siffofi ne kurum na itace da na dutse, da mutane suka yi da hannuwansu.

20. Yanzu dai, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga Assuriyawa domin dukan al'umman duniya su sani kai ne Allah kai kaɗai.”

21. Sa'an nan Ishaya ya aiki manzo zuwa wurin sarki Hezekiya, ya faɗa masa amsar Ubangiji a kan addu'ar sarki.

22. Ubangiji ya ce, “Birnin Urushalima yana yi maka dariya, kai Sennakerib, yana kuma yi maka ba'a.

23. Wa kake tsammani kana raina, kana yi masa ba'a? Ba ka ba ni girma ba, ni Allah mai tsarki na Isra'ila.

24. Ka aike da barorinka don su yi mini fāriya, da cewa ka ci nasara da duwatsu mafi tsayi da karusanka, har da ƙwanƙolin Dutsen Lebanon. Kana fāriya da cewa a can ka sare dogayen itatuwan al'ul da na fir, ka kuma kai wuri mafi nisa na jeji.

25. Ka kuma yi fāriya da cewa ka haƙa rijiyoyi a baƙuwar ƙasa, ka kuma sha ruwansu, sojojinka kuma sun tattake Kogin Nilu da ƙafafunsu, har ya ƙafe.

26. “Ba ka taɓa sani, na riga na shirya a yi haka tuntuni ba? Yanzu ne kuwa na cika wannan. Ni na ba ka iko ka ragargaza birane masu kagarai su zama tsibin ɓuraguzai.

27. Mutanen da suke zaune a can marasa ƙarfi ne. Sun firgita, sun suma. Sun zama kamar ciyawa a saura, ko hakukuwan da suka tsiro a kan rufi, waɗanda zafin iskar gabas ta buga su.

28. “Amma na san kome game da kai, abin da kake yi da inda kake tafiya. Na san yadda ka harzuƙa gāba da ni.

29. Na sami labarin irin harzuƙarka da girmankanka, yanzu kuwa zan sa ƙugiya a hancinka, linzami kuma a bakinka, in komar da kai.”

30. Sa'an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Ga alama a kan abin da zai faru. Da bana da baɗi sai gyauro za ku ci, amma a shekara ta biye za ku iya shuka hatsi ku kuma girbe shi, ku dasa kurangar inabi ku ci 'ya'yan.

31. Su da suka tsira daga al'ummar Yahuza za su yi lafiya kamar dashe-dashen da saiwoyinsu suka shiga da zurfi cikin ƙasa, suka kuma ba da amfani.

32. Mutanen da za su tsira su ne na cikin Urushalima da na kan Dutsen Sihiyona, gama Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyya ya sa haka ya faru.

33. “Wannan shi ne abin da Ubangiji ya ce a kan Sarkin Assuriya, ‘Ba zai shiga wannan birni ba, ko kuwa ya harba ko da kibiya ɗaya a cikinsa. Sojoji masu garkuwoyi ba za su zo ko kusa da birnin ba, ba kuma za su yi mahaurai kewaye da birnin ba.

34. Zai koma ta kan hanyar da ya zo, ba kuwa zai taɓa shiga wannan birni ba. Ni, Ubangiji, ni na faɗa.

35. Zan kāre wannan birni in kiyaye shi, saboda girmana, domin kuma alkawarin da na yi wa bawana Dawuda.’ ”

36. Mala'ikan Ubangiji kuwa ya shiga sansanin Assuriyawa ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar (185,000). Da asuba ta yi, sai ga su can kwankwance, duk sun mutu!

37. Sa'an nan sai Sarkin Assuriya, wato Sennakerib, ya janye ya koma Nineba.

38. Wata rana ya je yana sujada a gidan gunkinsa Nisrok, sai biyu daga cikin 'ya'yansa, Adrammelek da Sharezer, suka kashe shi da takubansu, sa'an nan suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Wani daga cikin sauran 'ya'yansa, wato Esar-haddon, ya gāje shi ya zama sarki.