Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Waƙar Godiya

1. Rana tana zuwa sa'ad da jama'a za su raira waƙa, su ce,“Ina yabonka ya Ubangiji! A dā ka yi fushi da ni,Amma yanzu kana yi mini ta'aziyya, ba za ka ƙara yin fushi da ni ba.

2. Allah ne Mai Cetona,Zan dogara gare shi, ba zan ji tsoro ba.Ubangiji ne yake ba ni iko da ƙarfi,Shi ne Mai Cetona.”

3. Kamar yadda ruwan daɗi yake sa mai jin ƙishirwa farin ciki,Haka nan jama'ar Allah suke farin ciki sa'ad da ya cece su.

4. A wannan rana jama'a za su raira waƙa, su ce,“Ku yi wa Ubangiji godiya! Ku nemi taimako a gare shi!Ku faɗa wa dukan sauran al'umma abin da ya aikata!Ku faɗa musu irin girman da yake da shi!

5. Ku raira waƙa ga Ubangiji, saboda manyan ayyuka da ya aikata.Bari dukan duniya ta ji labarin.

6. Bari dukan waɗanda suke zaune a Sihiyona su yi sowa su raira waƙa!Gama Mai Tsarki, Allah na Isra'ila, mai girma ne,Yana zaune tare da mutanensa.”