Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42
  43. 43
  44. 44
  45. 45
  46. 46
  47. 47
  48. 48
  49. 49
  50. 50
  51. 51
  52. 52
  53. 53
  54. 54
  55. 55
  56. 56
  57. 57
  58. 58
  59. 59
  60. 60
  61. 61
  62. 62
  63. 63
  64. 64
  65. 65
  66. 66

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Annabci a kan Habasha

1. A hayin kogunan Habasha akwai wata ƙasa inda ake jin amon fikafikai.

2. Daga waccan ƙasar wakilai sukan gangaro daga Kogin Nilu a cikin jiragen ruwa da aka yi da iwa. Ku koma gida, ku manzanni masu gaggawa! Ku kai saƙo ƙasarku, can a mafarin Kogin Nilu, zuwa ga al'ummarku mai ƙarfi mai iko, zuwa ga dogayen mutanenku masu sulɓin jiki, waɗanda ake jin tsoronsu ko'ina a duniya.

3. Kowane mutum da yake a duniya ya kasa kunne, kowannen da yake zaune a duniya, ya duba tutar, alama da za a ɗaga sama a ƙwanƙolin duwatsu, ya kasa kunne ga busar ƙaho!

4. Ubangiji ya ce mini “Zan duba daga samaniya a hankali kamar yadda raɓa take saukowa a natse da gumin dare a lokacin girbi, hasken rana kuma a yini.

5. Kafin a tattara 'ya'yan inabi, sa'ad da furanni duka suka karkaɗe, 'ya'yan inabi suna ta nuna, haka magabta za su hallaka Habasha a sawwaƙe kamar yadda ake faffalle rassan kurangar inabi da wuƙa.

6. Za a bar gawawwakin sojojinsu a fili domin tsuntsaye da namomin jeji su zama abincin tsuntsaye da bazara, abincin namomin jeji kuma a lokacin sanyi.”

7. A wannan lokaci Ubangiji Mai Runduna zai karɓi hadayu daga wannan ƙasa, a mafarin Kogin Nilu, wato wannan ƙaƙƙarfar al'umma mai iko, waɗannan dogayen mutane masu sulɓin jiki, waɗanda ake jin tsoronsu ko'ina a duniya. Za su zo Dutsen Sihiyona, inda ake yi wa Ubangiji Mai Runduna sujada.