Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 14:11-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Sai Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu'a domin lafiyar jama'an nan.

12. Ko da sun yi azumi, ba zan ji kukansu ba, ko da sun miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta sha, ba zan karɓe su ba. Amma zan hallaka su da takobi, da yunwa, da annoba.”

13. Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah, ga shi, annabawa sun faɗa musu, sun ce, ‘Ba za ku ga takobi ko yunwa ba, amma zan ba ku dawwamammiyar salama a wannan wuri.’ ”

14. Ubangiji kuwa ya ce mini, “Annabawa, annabcin ƙarya suka yi da sunana. Ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba, ban kuma yi magana da su ba. Annabcin da suke yi muku na wahayin ƙarya ne, dubar da suke yi marar amfani ce, tunaninsu ne kawai.

15. Domin haka ga abin da ni Ubangiji na ce a kan annabawan da suke yin annabci da sunana, ko da yake ban aike su ba, waɗanda suke cewa, ‘Takobi da yunwa ba za su shigo ƙasan nan ba.’ Za a hallaka su da takobi da yunwa.

16. Mutanen da suka yi wa annabci, za a jefar da su waje a kan titunan Urushalima, a karkashe su da yunwa da takobi, ba wanda zai binne su, da su, da matansu, da 'ya'yansu mata da maza. Zan sa muguntarsu ta koma kansu.

17. “Irmiya, ka faɗa wa mutanen baƙinciki da ya same ka,Ka ce, ‘Bari idanuna su yi ta zub dahawaye dare da rana,Kada su daina, saboda an bugebudurwa, 'yar jama'ata,An yi mata babban rauni da dūkamai tsanani.

Karanta cikakken babi Irm 14