Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 8:25-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Na auna musu azurfa, da zinariya, da kwanoni waɗanda sarki da fādawansa, da manyan mutanensa, da Isra'ilawa duka suka kawo suka miƙa domin Haikalin Allahnmu.

26-27. Ga abin da na auna na ba su,talanti ɗari shida da hamsin na azurfakayan azurfa na talanti ɗarikayan zinariya na talanti ɗarikwanonin zinariya guda ashirin na darik dubu (1,000)kwanoni guda biyu na tatacciyar tagulla, darajarsu daidai da kwanon zinariya.

28. Na ce musu, “Ku tsarkaka ne ga Ubangiji, kayayyakin kuma tsarkaka ne, azurfa da zinariya sadaka ce ta yardar rai ga Ubangiji Allah na kakanninku.

29. Ku riƙe su, ku yi tsaronsu, har lokacin da za ku kai su a gaban manyan firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin gidajen kakanninku na Isra'ila a Urushalima, a shirayin Haikalin Ubangiji.”

30. Sai firistoci da Lawiyawa suka ɗauki azurfa, da zinariya, da kwanoni waɗanda aka auna, zuwa Urushalima, zuwa Haikalin Allahnmu.

31. Muka kuwa tashi daga kogin Ahawa a ran goma sha biyu ga watan ɗaya, don mu tafi Urushalima, Allahnmu kuma yana tare da mu, ya kuwa cece mu daga hannun maƙiyanmu, da mafasa a hanya.

32. Muka iso Urushalima, muka yi kwana uku.

33. A rana ta huɗu, a Haikalin Allah, sai aka ba da azurfa, da zinariya, da kwanoni ga Meremot ɗan Uriya, firist, da Ele'azara ɗan Finehas, da Lawiyawa, wato Yozabad ɗan Yeshuwa, da Nowadiya ɗan Binnuyi.

34. Aka ƙidaya dukan kome aka kuma auna, sa'an nan aka rubuta yawan nauyin.

35. Waɗanda fa suka komo daga zaman talala, suka miƙa wa Allah na Isra'ila hadaya ta ƙonawa, da bijimai goma sha biyu domin dukan Isra'ila,da raguna tasa'in da shida, da 'yan raguna saba'in da bakwai. Suka kuma miƙa hadaya don zunubi da bunsurai goma sha biyu. Dukan wannan ya zama hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.

36. Suka faɗa wa wakilan sarki da masu mulkin Yammacin Kogin Yufiretis umarnan sarki. Su kuwa suka taimaki mutane, da kuma Haikalin Allah.

Karanta cikakken babi Ezra 8