Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Yawan Kamammu da suka Komo.

1. Waɗannan su ne mutanen da suka bar lardin Babila suka komo Urushalima da Yahuza daga bautar talala da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kai su Babila. Kowa ya koma garinsu.

2. Sun komo tare da Zarubabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Seriya, da Re'elaya, da Mordekai, da Bilshan, Misfar, da Bigwai, da Rehun, da Ba'ana.Ga jerin iyalan Isra'ila, da yawan waɗanda suka komo na kowane iyali daga zaman talala.

3-20. Zuriyar Farosh, mutum dubu biyu da ɗari da saba'in da biyu (2,172)Zuriyar Shefatiya, mutum ɗari uku da saba'in da biyuZuriyar Ara,mutum ɗari bakwai da saba'in da biyarZuriyar Fahat-mowab na zuriyar Yeshuwa da Yowab, mutum dubu biyu da ɗari takwas da goma sha biyu (2,812)Zuriyar Elam, mutum dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)Zuriyar Zattu, mutum ɗari tara da arba'in da biyarZuriyar Zakkai, mutum ɗari bakwai da sittinZuriyar Bani, mutum ɗari shida da arba'in da biyuZuriyar Bebai, mutum ɗari shida da ashirin da ukuZuriyar Azgad, mutum dubu da ɗari biyu da ashirin da biyu (1,222)Zuriyar Adonikam, mutum ɗari shida da sittin da shidaZuriyar Bigwai, mutum dubu biyu da hamsin da shida (2,056)Zuriyar Adin, mutum ɗari huɗu da hamsin da huɗuZuriyar Ater na Hezekiya, mutum tasa'in da takwasZuriyar Bezai, mutum ɗari uku da ashirin da ukuZuriyar Yora, mutum ɗari da goma sha biyuZuriyar Hashum, mutum ɗari biyu da ashirin da ukuZuriyar Gibeyon, mutum tasa'in da biyar

21-35. Mutanen da suke a garuruwan nan, su ma suka komo.Mutanen Baitalami, mutum ɗari da ashirin da ukuMutanen Netofa, mutum hamsin da shidaMutanen Anatot, mutum ɗari da ashirin da takwasZuriyar Azmawet, mutum arba'in da biyuZuriyar Kiriyat-yeyarim, da Kefira, da Biyerot, mutum ɗari bakwai da arba'in da ukuZuriyar Rama da Geba, mutum ɗari shida da ashirin da ɗayaMutanen Mikmash, mutum ɗari da ashirin da biyuMutanen Betel da Ai, mutum ɗari biyu da ashirin da ukuZuriyar Nebo, mutum hamsin da biyuZuriyar Magbish, mutum ɗari da hamsin da shidaZuriyar wancan Elam, mutum dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)Zuriyar Harim, mutum ɗari uku da ashirinZuriyar Lod, da Hadid, da Ono, mutum ɗari bakwai da ashirin da biyarMutanen Yariko, mutum ɗari uku da arba'in da biyarZuriyar Senaya, mutum dubu uku da ɗari shida da talatin (3,630)

36-39. Ga kuma lissafin iyalan firistocin da suka komo,Zuriyar Yedaiya na gidan Yeshuwa, mutum ɗari da saba'in da ukuZuriyar Immer, mutum dubu da hamsin da biyu (1,052)Zuriyar Fashur,mutum dubu da ɗari biyu da arba'in da bakwai (1,247)Zuriyar Harim, mutum dubu da goma sha bakwai (1,017)

40. Lawiyawa na zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel na Hodawiya mutum saba'in da huɗu.

41. Mawaƙa na zuriyar Asaf, mutum ɗari da ashirin da takwas.

42. Zuriyar Shallum, da ta Ater, da ta Talmon, da ta Akkub, da ta Hatita, da ta Shobai, su ne zuriyar matsaran ƙofa, yawan mutanensu duka ɗari da talatin da tara.

43-54. Ga lissafin ma'aikatan Haikali da suka komo.Zuriyar Ziha, da zuriyar Hasufa, da zuriyar TabbawotZuriyar Keros, da zuriyar Siyaha, da zuriyar FadonZuriyar Lebana, da zuriyar Hagaba, da zuriyar AkkubZuriyar Hagab, da zuriyar Shamlai, da zuriyar HananZuriyar Giddel, da zuriyar Gahar, da zuriyar RewaiyaZuriyar Rezin,da zuriyar Nekoda, da zuriyar GazamZuriyar Ussa, da zuriyar Faseya, da zuriyar BesaiZuriyar Asna, da Me'uniyawa, da NefushiyawaZuriyar Bakbuk, da zuriyar Hakufa da zuriyar HarhurZuriyar Bazlut, da zuriyar Mehida, da zuriyar HarshaZuriyar Barkos, da zuriyar Sisera, da zuriyar TemaZuriyar Neziya, da zuriyar Hatifa

55-57. Zuriyar barorin Sulemanu, su neZuriyar Sotai, da zuriyar Hassoferet, da zuriyar FerudaZuriyar Yawala, da zuriyar Darkon, da zuriyar GiddelZuriyar Shefatiya, da zuriyar Hattil, da zuriyar Fokeret-hazzebayim, da zuriyar Ami

58. Dukan zuriyar ma'aikatan Haikali da zuriyar barorin Sulemanu su ɗari uku da tasa'in da biyu ne.

59. Waɗannan su ne waɗanda suka zo daga Tel-mela, da Tel-harsha, da Kerub, da Addan, da Immer, amma ba su iya tabbatar da gidajen kakanninsu da asalinsu ba, ko su na Isra'ila ne.

60. Su ne zuriyar Delaiya, da zuriyar Tobiya, da zuriyar Nekoda. Su ɗari shida da hamsin da biyu ne.

61. Sai kuma zuriyar firistoci, wato zuriyar Habaya, da zuriyar Hakkoz, da zuriyar Barzillai, wanda ya auri mata daga cikin 'ya'yan Barzillai, mata, mutumin Gileyad, aka kira shi da sunnansu,

62. suka bincika littafin asalin kakanninsu, amma suka ga ba su a ciki. Don haka aka mai da su ƙazantattu, ba a yarda musu su yi aikin firist ba.

63. Sai mai mulki ya ce ba za su ci abinci mafi tsarki ba, sai firist ya shawarci Urim da Tummim tukuna, wato kamar kuri'a ke nan.

64-67. Yawan taron jama'a su dubu arba'in da biyu da ɗari uku da sittin (42,360).Barorinsu maza da mata, dubu bakwai da ɗari uku da talatin da bakwai (7,337)Mawaƙa ɗari biyu mata da mazaDawakansu ɗari bakwai da talatin da shidaAlfadaransu ɗari biyu da arba'in da biyarRaƙumansu kuma ɗari huɗu da talatin da biyar neJakunansu kuwa dubu shida da ɗari bakwai da ashirin (6,720)

68. Waɗansu shugabannin gidajen kakanninsu, sa'ad da suka isa Haikalin Ubangiji a Urushalima, sai suka bayar da kyautai da yardar rai don a sāke gina Haikalin Ubangiji a wurin da yake dā.

69. Gwargwadon arzikinsu suka ba da darik dubu sittin da dubu ɗaya (61,000) na zinariya, da maina dubu biyar (5,000) na azurfa, da tufafin firistoci guda ɗari.

70. Firistoci, da Lawiyawa, da waɗansu mutanen da suke zaune a Urushalima da kewayenta, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da ma'aikatan Haikalin, da dukan mutanen Isra'ila suka zauna a garuruwansu.