Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

An Shirya yadda Za a Rabu da Aurayya da Arna

1. Sa'ad da Ezra yake yin addu'a, yana hurta laifi, yana kuka, yana a durƙushe gaban Haikalin Allah, sai babban taron jama'a, mata, da maza, da yara daga Isra'ila suka taru wurinsa. Mutane suka yi kuka mai zafi.

2. Sai Shekaniya ɗan Yehiyel, daga zuriyar Elam, ya yi wa Ezra magana, ya ce, “Mun yi wa Allahnmu rashin aminci, gama mun auri mata baƙi daga mutanen ƙasar, amma duk da haka akwai sauran bege ga Isra'ila.

3. Bari mu yi alkawari da Allahnmu, mu kori dukan waɗannan mata da 'ya'yansu, bisa ga shawarar shugabanni da waɗanda suke rawar jiki saboda umarnin Allah. Bari mu yi alkawari bisa ga doka.

4. Sai ka tashi, gama wannan hakkinka ne, mu kuwa muna tare da kai. Sai dai ka yi ƙarfin hali, ka yi shi.”

5. Ezra kuwa ya tashi, ya sa firistoci da suke shugabanni, da Lawiyawa, da dukan mutanen Isra'ila su rantse, cewa za su yi abin da aka ce. Sai suka yi rantsuwar.

6. Sa'an nan Ezra ya tashi daga Haikalin Allah, ya tafi gidan Yohenan ɗan Eliyashib, amma ko da ya tafi can bai ci abinci ba, bai kuma sha ruwa ba, gama yana baƙin ciki saboda rashin aminci na waɗanda suka dawo daga zaman talala.

7. Sai aka yi shela a dukan Yahuza da Urushalima, cewa dukan waɗanda suka komo daga zaman talala, su hallara a Urushalima.

8. Duk wanda bai zo a cikin kwana uku ba, za a washe shi, a kuma ware shi daga jama'ar da suka dawo daga zaman talala. Haka shugabanni da dattawa suka umarta.

9. Sai dukan mutanen Yahuza da na Biliyaminu, suka hallara a Urushalima kafin kwana uku, a ran ashirin ga watan tara. Mutanen suka zauna a dandalin Haikali, suna rawar jiki saboda al'amarin, da kuma saboda babban ruwan sama.

10. Ezra firist kuwa ya miƙe tsaye ya ce wa jama'a, “Kun yi rashin aminci, kun auri mata baƙi, ta haka kuka ƙara zunubin Isra'ila.

11. Yanzu sai ku hurta wa Ubangiji Allah na kakanninku, laifinku, ku kuma aikata nufinsa. Ku ware kanku daga mutanen ƙasar da mata baƙi.”

12. Dukan taron jama'a suka amsa da babbar murya, suka ce, “Haka nan ne, haka nan ne, dole ne mu yi yadda ka faɗa.

13. Amma mutane suna da yawa, a lokacin kuwa ana marka, ba za mu iya tsayawa a fili ba, aikin nan kuma ba na kwana ɗaya, ko biyu ba ne, gama mun yi laifi sosai wajen wannan al'amari.

14. Bari shugabanninmu su wakilci dukan taron jama'a, bari kuma dukan waɗanda suke garuruwanmu da suka auri mata baƙi su zo a ƙayyadadden lokaci tare da dattawa da alƙalan garuruwansu, har lokacin da Allah ya huce daga fushinsa a kanmu saboda al'amarin nan.”

15. Jonatan ɗan Asahel da Yazeya ɗan Tikwa ne kaɗai ba su yarda da wannan ba, Meshullam da Shabbetai suka goyi bayansu.

16. Waɗanda suka komo daga zaman talala kuwa suka yi haka. Sai Ezra firist ya zaɓi mutanen da suke shugabannin gidajen kakanninsu. Aka rubuta sunan kowa. Sai suka taru ran ɗaya ga watan goma, don su bincika al'amarin.

17. Suka gama binciken dukan mutanen da suka auri mata baƙi ran ɗaya ga watan fari.

Mazajen da Suke da Mata Baƙi

18. Ma'aseya, da Eliyezer, da Yarib, da Gedaliya iyalin Yeshuwa ɗan Yehozadak, su ne firistocin da suka auri mata baƙi.

19. Sai suka yi alkawari, cewa za su saki matansu. Suka ba da rago don yin hadaya saboda laifinsu.

20-24. Na iyalin Immer, Hanani, da ZabadiyaNa iyalin Harim, Ma'aseya, da Iliya, da Shemaiya, da Yehiyel, da UzziyaNa iyalin Fashur, Eliyehoyenai, da Ma'aseya, da Isma'ilu, da Netanel, da Yozabad, da ElasaNa Lawiyawa, Yozabad, da Shimai, da Kelaya, wato Kelita, da Fetahiya, da Yahuza, da EliyezerNa mawaƙa, EliyashibNa masu tsaron ƙofa, Shallum, da Telem, da Uri

25-33. Akwai kuma waɗansu na Isra'ila.Na iyalin Farosh, Ramiya, da Izziya, da Malkiya, da Miyamin, da Ele'azara, da Malkiya, da BenaiyaNa iyalin Elam, Mattaniya, da Zakariya, da Yehiyel, da Abdi, da Yeremot, da IliyaNa iyalin Zattu, Eliyehoyenai, da Eliyashib, da Mattaniya, da Yeremot, da Zabad, da AzizaNa iyalin Bebai, Yehohanan,da Hananiya, da Zabbai, da AtlaiNa iyalin Bani, Meshullam, da Malluki, da Adaya, da Yashub, da Sheyal, da YeremotNa iyalin Fahat-mowab, Adana, da Kelal, da Benaiya, da Ma'aseya, da Mattaniya, da Bezalel, da Binnuyi, da ManassaNa iyalin Harim, Eliyezer, da Isshiya, da Malkiya, da Shemaiya, da Shimeyon, da Biliyaminu, da Malluki, da ShemariyaNa iyalin Hashum, Mattenai, da Mattatta, da Zabad, da Elifelet, da Yeremai, da Manassa, da Shimai

34-37. Na iyalin Bani, Mayadi, da Amram, da Yuwel, da Benaiya, da Bedeya, da Keluhi, da Waniya, da Meremot, da Eliyashib, da Mattaniya, da Mattenai, da Yawasu

38-42. Na iyalin Binnuyi, Shimai, da Shelemiya, da Natan, da Adaya, da Maknadebai, da Shashai, Sharai, da Azarel, da Shelemiya, da Shemariya, da Shallum, da Amariya, da Yusufu

43. Na iyalin Nebo, Yehiyel, da Mattitiya, da Zabad, da Zebina, da Yaddai, da Yowel, da Benaiya

44. Waɗannan duk sun auro mata baƙi. Sai suka sake su da 'ya'yansu.