Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 2:21-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Mutanen da suke a garuruwan nan, su ma suka komo.Mutanen Baitalami, mutum ɗari da ashirin da ukuMutanen Netofa, mutum hamsin da shidaMutanen Anatot, mutum ɗari da ashirin da takwasZuriyar Azmawet, mutum arba'in da biyuZuriyar Kiriyat-yeyarim, da Kefira, da Biyerot, mutum ɗari bakwai da arba'in da ukuZuriyar Rama da Geba, mutum ɗari shida da ashirin da ɗayaMutanen Mikmash, mutum ɗari da ashirin da biyuMutanen Betel da Ai, mutum ɗari biyu da ashirin da ukuZuriyar Nebo, mutum hamsin da biyuZuriyar Magbish, mutum ɗari da hamsin da shidaZuriyar wancan Elam, mutum dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)Zuriyar Harim, mutum ɗari uku da ashirinZuriyar Lod, da Hadid, da Ono, mutum ɗari bakwai da ashirin da biyarMutanen Yariko, mutum ɗari uku da arba'in da biyarZuriyar Senaya, mutum dubu uku da ɗari shida da talatin (3,630)

Karanta cikakken babi Ezra 2

gani Ezra 2:21-35 a cikin mahallin