Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ezra 8:20-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Da kuma ma'aikatan Haikali mutum ɗari biyu da ashirin, waɗanda Dawuda da ma'aikatansa suka keɓe domin su taimaki Lawiyawa. Aka ambaci waɗannan da sunayensu.

21. Na kuma yi shelar azumi a bakin rafin Ahawa don mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu roƙe shi ya kiyaye mu, da 'ya'yanmu, da kayanmu a hanya.

22. Gama na ji kunya in roƙi sarki ya ba mu sojojin ƙasa da na doki su kāre mu daga maƙiya a hanya, da yake na riga na faɗa masa cewa, “Allah yana tare da dukan waɗanda suke nemansa, ikonsa da fushinsa mai zafi kuwa yana kan dukan waɗanda suke mantawa da shi.”

23. Don haka muka yi azumi, muka roƙi Allah saboda wannan, shi kuwa ya ji roƙonmu.

24. Sai na keɓe goma sha biyu daga cikin manyan firistoci, wato Sherebiya, da Hashabiya, da waɗansu goma daga cikin danginsu.

25. Na auna musu azurfa, da zinariya, da kwanoni waɗanda sarki da fādawansa, da manyan mutanensa, da Isra'ilawa duka suka kawo suka miƙa domin Haikalin Allahnmu.

26-27. Ga abin da na auna na ba su,talanti ɗari shida da hamsin na azurfakayan azurfa na talanti ɗarikayan zinariya na talanti ɗarikwanonin zinariya guda ashirin na darik dubu (1,000)kwanoni guda biyu na tatacciyar tagulla, darajarsu daidai da kwanon zinariya.

28. Na ce musu, “Ku tsarkaka ne ga Ubangiji, kayayyakin kuma tsarkaka ne, azurfa da zinariya sadaka ce ta yardar rai ga Ubangiji Allah na kakanninku.

29. Ku riƙe su, ku yi tsaronsu, har lokacin da za ku kai su a gaban manyan firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin gidajen kakanninku na Isra'ila a Urushalima, a shirayin Haikalin Ubangiji.”

30. Sai firistoci da Lawiyawa suka ɗauki azurfa, da zinariya, da kwanoni waɗanda aka auna, zuwa Urushalima, zuwa Haikalin Allahnmu.

31. Muka kuwa tashi daga kogin Ahawa a ran goma sha biyu ga watan ɗaya, don mu tafi Urushalima, Allahnmu kuma yana tare da mu, ya kuwa cece mu daga hannun maƙiyanmu, da mafasa a hanya.

32. Muka iso Urushalima, muka yi kwana uku.

Karanta cikakken babi Ezra 8