Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ez 33:2-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. “Ɗan mutum, ka yi magana da mutanenka, ka faɗa musu cewa, ‘Idan na zare takobi a kan wata ƙasa, idan mutanen ƙasar suka ɗauki wani mutum daga cikinsu, suka sa shi ya zama ɗan tsaronsu,

3. idan ya ga an taso wa ƙasar da takobi, sai ya busa ƙaho don ya faɗakar da jama'ar.

4. Idan wani ya ji amon ƙahon, amma bai kula ba, har takobin ya zo ya kashe shi, hakkin jininsa yana bisa kansa.

5. Gama ya ji amon ƙahon, bai kuwa kula ba, hakkin jininsa zai zauna a bisa kansa. Amma idan ya kula da faɗakar, zai tsira da ransa.

6. Idan kuwa ɗan tsaron ya ga takobi yana zuwa, amma bai busa ƙahon don ya faɗakar da mutanen ba, takobin kuwa ya zo, ya kashe wani daga cikinsu, shi wanda aka kashe ya mutu saboda laifinsa, amma zan nemi hakkin jininsa daga hannun ɗan tsaron.’

7. “Yanzu fa, kai ɗan mutum, na sa ka zama ɗan tsaro a al'ummar Isra'ila. Duk lokacin da ka ji magana daga bakina, sai ka faɗakar da su.

8. Idan na hurta, cewa hakika mugu zai mutu, amma ba ka faɗakar da shi don ya juyo, ya bar muguwar hanyarsa ba, wannan mugun zai mutu saboda laifinsa, amma zan nemi hakkin jininsa a hannunka.

9. Amma idan ka faɗakar da mugu don ya juyo, ya bar muguwar hanyarsa, idan bai juyo ya bar muguwar hanyarsa ba, zai mutu saboda laifinsa, amma za ka tsira da ranka.”

10. “Kai ɗan mutum, sai ka faɗa wa mutanen Isra'ila, ‘Kuna cewa, “Laifofinmu da zunubanmu suna nawaita mana, muna kuwa lalacewa, yanzu fa, ta ƙaƙa za mu rayu?” ’

11. Ka faɗa musu, ni Ubangiji Allah, na ce, ‘Hakika, ba na murna da mutuwar mugu, amma na fi so mugun ya bar hanyarsa ya rayu. Ku juyo, ku juyo daga mugayen hanyoyinku, gama don me za ku mutu, ya mutanen Isra'ila?’

12. “Ɗan mutum, sai kuma ka faɗa wa mutanenka, cewa adalcin adali ba zai cece shi ba sa'ad da ya yi laifi, muguntar mugu kuma ba za ta sa ya mutu ba idan ya bar muguntarsa. Adalcin adali ba zai cece shi ba, idan ya shiga aikata zunubi.

13. Idan na ce wa adali, ba shakka zai rayu, amma idan ya dogara ga adalcin da ya riga ya yi, sa'an nan ya shiga aikata laifi, ba za a tuna da ayyukan adalcinsa na dā ba. Zai mutu saboda laifin da ya yi.

14. Idan kuma na ce wa mugu ba shakka zai mutu, amma idan ya bar laifinsa, ya shiga aikata adalci,

15. idan kuma ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya ƙwace, sa'an nan ya kiyaye dokokin rai, ya daina yin laifi, hakika, zai rayu, ba zai mutu ba.

Karanta cikakken babi Ez 33