Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Dan 9:19-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Ya Ubangiji, ka ji mu. Ya Ubangiji, ka garfarce mu. Ya Ubangiji, ka saurare mu, ka yi wani abu saboda sunanka. Ya Allahna, kada ka yi jinkiri domin da sunanka ake kiran birninka da jama'arka.”

20. Sa'ad da nake ta addu'a, ina faɗar zunubina, da na jama'ata Isra'ila, ina kawo roƙe-roƙena wurin Ubangiji Allahna saboda tsattsarkan tudun Allahna.

21. Sa'ad da nake yin addu'a, sai mutumin nan Jibra'ilu, wanda na gani a wahayin da ya wuce, ya zo wurina a gaggauce wajen lokacin yin hadaya ta maraice.

22. Ya zo, ya ce mini, “Ya Daniyel, na zo ne don in ba ka hikima da ganewa.

23. A lokacin da ka fara roƙe-roƙenka sai aka ba da umarni, na kuwa zo domin in faɗa maka, gama ana sonka ƙwarai. Sai ka fahimci maganar da wahayin.

24. “An ƙayyade wa jama'arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa'in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa'an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake Haikali.

25. Sai ka sani, ka kuma gane, daga lokacin da aka umarta a sāke gina Urushalima har zuwa lokacin da shugaba, Masiha, zai zo, za a yi shekara arba'in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da kagara.

26. Za ta kasance har shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, sa'an nan za a kashe Masihan, ba zai sami kome ba. Jama'ar shugaban da zai zo za su hallaka birnin da Haikali. A ƙarshensa za a yi rigyawa, da yaƙe-yaƙe, da hallakarwa kamar yadda aka ƙaddara.

27. Wannan shugaba zai yi alkawari mai ƙarfi na shekara bakwai da mutane da yawa. Amma bayan shekara uku da rabi za a hana a yi sadaka da hadaya. Abin ƙyama zai kasance a ƙwanƙolin Haikali, har lokacin da ƙaddara za ta auko wa wanda ya sa abin ƙyama.”

Karanta cikakken babi Dan 9