Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Ayuba Yana Marmarin Kai Ƙara Gaban Allah

1. Ayuba ya amsa.

2. “Duk da haka zan yi tawaye in yi wa Allah gunaguni,In dinga yin nishi.

3. Da ma na san inda zan same shi,In kuma san yadda zan kai wurinsa,

4. Da zan kai ƙarata a gare shi, in faɗa masa duk muhawarata, in kāre kaina ne.

5. Ina so in san irin amsar da zai mayar mini,Ina kuma so in san yadda zai amsa mini.

6. Allah kuwa da dukan ƙarfinsa zai yi gāba da ni?A'a, zai saurara in na yi magana.

7. Ina da aminci, zan faɗa wa Allah ra'ayina,Zai tabbatar da amincina duka.

8. “Na nemi Allah a gaba, amma ban same shi a can ba,Ban kuwa same shi a baya ba sa'ad da na neme shi.

9. Allah ya tafi wurin aiki a dama,Ya kuma tafi hagu, amma har yanzu ban gan shi ba.

10. Duk da haka Allah ya san kowane irin hali da nake ciki.Idan ya jarraba ni zai tarar ni tsattsarka ne.

11. Da aminci ina bin hanyar da ya zaɓa,Ban kuwa taɓa kaucewa daga wannan gefe zuwa wancan ba.

12. A kullum ina aikata abin da Allah ya umarta,Ina bin nufinsa, ba nufin kaina ba.

13. “Bai taɓa sākewa ba. Ba wanda zai iya gāba da shi,Ko kuma ya hana shi yin abin da yake so ya aikata.

14. Zai tabbatar da abin da ya shirya domina,Wannan ma ɗaya daga cikin shirye-shiryen da ya yi ne.

15. Don haka in rawar jiki a gabansa saboda tsoro.

16. Allah Mai Iko Dukka ya lalatar da ƙarfin halina.Allah ne ya tsorata ni,

17. Amma ban damu da damu ba,Ko da yake duhu ya dunɗe idanuna.”