Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Samun Hikima Yana da Wuya

1. “Hakika akwai ma'adinai na azurfa,Da wuraren da ake tace zinariya.

2. Mutane sukan haƙo baƙin ƙarfe daga ƙasa,Sukan narkar da tagulla daga dutse.

3. Mutane sukan kawar da duhu,Sukan kuma bincike zuzzurfar iyaka,Sukan haƙo duwatsun da suke cikin duhu, duhu baƙi ƙirin.

4. Sukan haƙa loto a fadama nesa da mutane,Sukan kafa abin lilo su yi ta lilo nesa da mutane.

5. “Daga cikin ƙasa ake samun abinci,Amma a ƙarƙashinta yakan zama kamar wuta.

6. Akwai duwatsu masu daraja cikin duwatsunta,Akwai zinariya a ƙurarta.

7. Tsuntsu mai cin nama bai san wannan hanya ba.Shaho ma bai gan ta ba.

8. Namomin jeji ba su taɓa bin hanyar ba,Ko zaki ma bai taɓa binta ba.

9. “Mutane sun iya sarrafa ƙanƙarar dutse,Suna kuma iya tumɓuke tushen duwatsu.

10. Sukan haƙa magudanar ruwa cikin duwatsu,Idanunsu sukan ga kowane abu mai daraja.

11. Sukan datse rafuffuka su hana su gudu,Su binciko abin da yake ɓoye, ya fito sarari.

12. Amma ina, a ina za a iya samun hikima?A ina za a samo haziƙanci?

13. Mutane ba su san darajar hikima ba,Ba a samunta a ƙasar masu rai.

14. Zurfafa sun ce, ‘Ba ta a cikinmu,’Tekuna kuma sun ce, ‘Ba ta tare da mu.’

15. Ba za a saye ta da zinariya tsantsa ba.Azurfa ba za ta iya biyan tamaninta ba.

16. Ko zinariyar Ofir, ko onis,Ko saffir, wato duwatsu masu daraja, ba za su iya biyan tamaninta ba.

17. Ba daidai take da zinariya ko madubi ba,Ba za a iya musayarta da kayayyakin da aka yi da zinariya tsantsa ba.

18. Kada ma a ko ambaci murjani,Da duwatsu masu walƙiya.Gama tamanin hikima ya fi na lu'ulu'ai mafiya daraja duka.

19. Ba za a daidaita tamaninta da na duwatsun tofaz na Habasha ba.Tamaninta ya fi na zinariya tsantsa.

20. “To, daga ina hikima ta fito?A wane wuri kuma haziƙanci yake?

21. Ba talikin da ya iya ganinta,Ko tsuntsun da yake tashi sama.

22. Halaka da Mutuwa sun ce,‘Da kunnuwanmu mun ji ƙishin-ƙishin a kanta.’

23. “Allah ne kaɗai ya san hanya zuwa gare ta,Ya san inda hikima take,

24. Saboda yana ganin duniya ɗungum,Yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sararin sama.

25. Sa'ad da Allah ya sa iska ta hura,Ya yi wa tekuna iyaka.

26. Sa'ad da ya ba da umarni ga ruwan sama,Da kuma hanyar da tsawa za ta bi,

27. Shi ya san hikimar, shi ya sanar,Ya tabbatar da ita, ya bincike ta sarai.

28. “Allah ya ce wa mutane,‘Duba, tsoron Ubangiji shi ne hikima,Rabuwa da mugunta kuma, ita ce haziƙanci.’ ”