Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34
  35. 35
  36. 36
  37. 37
  38. 38
  39. 39
  40. 40
  41. 41
  42. 42

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ayu 16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Ayuba Ya Yi Kukan abin da Allah Yake Yi

1. Ayuba ya yi magana.

2. “Ai, na taɓa jin magana irin wannan,Ta'aziyyar da kake yi azaba ce kawai.

3. Ka dinga yin magana ke nan har abada?A kullum maganarka ita ce dahir?

4. In da a ce a matsayina kake, ni kuma ina a naka,Ina iya faɗar duk abin da kake faɗa yanzu.Da sai in kaɗa kaina da hikima,In dulmuyar da kai a cikin rigyawar maganganu.

5. Da sai in ba ka shawara ta ƙarfafawa,In yi ta yi maka maganar ta'azantarwa.

6. “Amma ba abin da zan faɗa wanda zai taimaka,Yin shiru kuma ba zai raba ni da azaba ba.

7. Ka gajiyar da ni, ya Allah,Ka shafe iyalina.

8. Ka kama ni, kai maƙiyina ne.Na zama daga fata sai ƙasusuwa,Mutane suka ɗauka, cewa wannan ya tabbatar ni mai laifi ne.

9. Allah ya kakkarya gaɓoɓina da fushinsa,Yana dubana da ƙiyayya.

10. Mutane sun buɗe baki don su haɗiye niSuna kewaye ni suna ta marina.

11. Allah ya bashe ni ga mugaye.

12. Dā ina zamana da salama,Amma Allah ya maƙare ni,Ya fyaɗa ni ƙasa ya ragargaza ni.Allah ya maishe ni abin bārata.

13. Ya harbe ni da kibau daga kowane gefe.Kiban sun ratsa jikina sun yi mini rauni,Duk da haka bai nuna tausayi ba!

14. Ya yi ta yi mini rauni a kai a kai,Ya fāɗa mini kamar soja da ƙiyayya ta haukata.

15. “Ina makoki saye da tsummoki,Ina zaune cikin ƙura a kunyace.

16. Na yi ta kuka har fuskata ta zama ja wur,Idanuna kuma suka yi luhuluhu.

17. Amma ban yi wani aikin kama-karya ba,Addu'ata ga Allah kuwa ta gaskiya ce.

18. “Duniya, kada ki ɓoye laifofin da aka yi mini!Kada ki yi shiru da roƙon da nake yi na neman adalci!

19. Akwai wani a SamaWanda zai tsaya mini ya goyi bayana.

20. Ina so Allah ya ga hawayena,Ya kuma ji addu'ata.

21. “Ina so wanda zai yi roƙo ga Allah domina,Kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.

22. Yanzu shekaruna wucewa suke yi,Ina bin hanyar da ba a komawa.”