Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

2 Sam 12:12-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Kai, a ɓoye ka yi naka zunubi, amma zan sa a yi maka a gaban dukan mutanen Isra'ila da rana katā.’ ”

13. Sai Dawuda ya ce wa Natan, “Na yi wa Ubangiji zunubi.”Natan ya ce masa, “Ubangiji ya gafarta maka, ba za ka mutu ba.

14. Amma domin ka ba da ƙofa ga magabtan Ubangiji su zarge shi, wato saboda abin da ka aikata, ɗan da za a haifa maka zai mutu.”

15. Sa'an nan Natan ya tafi gida.Ubangiji kuwa ya sa ciwo ya kama yaron da matar Uriya ta haifa wa Dawuda.

16. Dawuda kuwa ya roƙi Allah saboda yaron. Ya yi azumi. Ya shiga ya kwanta a ƙasa dukan dare.

17. Sai fādawansa suka zo suka kewaye shi, don su tashe shi daga ƙasa, amma bai yarda ba, bai kuma ci abinci tare da su ba.

18. An kwana bakwai sai yaron ya mutu. Fādawansa suka ji tsoron faɗa masa rasuwar yaron. Suka ce wa junansu, “Ga shi, tun lokacin da yaron yake da rai mun yi masa magana, amma bai kasa kunne gare mu ba, yaya za mu iya faɗa masa rasuwar yaron? Zai yi wa kansa ɓarna.”

19. Da Dawuda ya ga fādawansa suna raɗa da juna, sai ya gane lalle yaron ya rasu. Ya tambaye su, ya ce, “Yaron ya rasu ne?”Suka amsa cewa, “I, ya rasu.”

20. Sai Dawuda ya tashi daga ƙasa, ya yi wanka, ya shafa mai, ya sake tufafinsa, ya tafi ɗakin sujada, ya yi sujada, sa'an nan ya koma gidansa ya ce a kawo abinci. Suka kawo masa abinci ya ci.

21. Fādawansa suka ce masa, “Me ka yi ke nan? Ka yi azumi, ka yi kuka saboda yaron tun yana da rai, amma da yaron ya rasu ka tashi, ka ci abinci.”

22. Ya ce musu, “Tun yaron yana da rai, na yi azumi da kuka, ina cewa wa ya sani, ko Ubangiji zai yi mini jinƙai, ya bar yaron da rai?

23. Amma yanzu ya rasu, me zai sa kuma in yi azumi? Zan iya koma da shi ne? Ni zan tafi wurinsa, amma shi ba zai komo wurina ba.”

24. Sa'an nan Dawuda ya yi wa Batsheba, matarsa, ta'aziyya. Ya shiga wurinta, ya kwana da ita. Ta haifa masa ɗa. Ya raɗa masa suna Sulemanu. Ubangiji kuwa ya ƙaunace shi,

25. ya kuma umarci annabi Natan ya raɗa wa yaron suna Yedideya, wato ƙaunataccen Ubangiji.

Karanta cikakken babi 2 Sam 12